Menu

SHUGABAN HUKUMAR NIMASA YA SHA ALWASHIN CIYAR DA HUKUMAR GABA

Admin 4 years ago

Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya sadaukar da lambar girmamawar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi ga masu ruwa da tsaki a bangaren iyakokin ruwan kasar bisa namijin kokarin da suke yi wajen ciyar da bangaren gaba.

A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin Ikko, yace Dr Bashir Yusuf Fagge ya bayyana hakan ne jim kadan bayan karban lambar girmamawar wanda aka yi a wannan mako a babban birnin tarayya, Abuja.

Dr Bashir Yusuf Jamoh ya kuma yabawa Ministan harkokin sufuri, Mu’azu Jaji Sambo da hukumar gudanarwar NIMASA dangane tsayin dakar da suke yi wajen habbaka bangaren iyakokin ruwan kasar nan, sannar ya sha alwashin kara bada himma sauke nauyin dake wuyan shi.

Shugaban hukumar har ila yau ya mika godiyar shi ga dukkan wadanda suka taya shi farin ciki bisa wannan wannan lambar girmamawa ta kasa da ya samu, inda ya ce wannan zai zaburar da shi wajen cigaba da yiwa kasa hidima.

A nashi bangaren, Ministan harkokin sufuri, Mu’azu Jaji Sambo yace babu shakka, Dr Bashir Jamoh ya cancanci samun wannan lambar girmamawa ta kasa dangane da sauye-sauyen da ya kawo tun bayan nada shi a matsayin Shugaban hukumar NIMASA da kuma kokarin shi wajen kare iyakokin ruwan kasar nan daga ayyukan mabarnata.

A nashi tsokacin, tsohon shugaban hukumar NIMASA, Dr Ade Dosunmu ya yaba da jajircewar Dr Bashir Jamoh ne wajen gudanar da aiki, sannan yace tabbas ya cancanta da samun wannan yabon girma.

Shi kuwa Sanata Danjuma La’ah yace jihar Kaduna da Al’ummar ta na alfahari da Dr Bashir Yusuf Jamoh.