Daga Nura Zazzau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin ƙasashen duniya wajen miƙa saƙon ta’aziyyarsa kan rasuwar fitaccen ɗan ƙwallon duniya Edson Arantes do Nascimento wanda aka fi sani da Pele.
Wannan na kunshene a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba shehu ya fitar, shugaba Buhari ya bayyana ɗan wasan da cewa mutum ne ”mai kirki da ƙanƙan da-kai, duk da cewa shi babban ɗan wasa ne”.
KARANTA WANNAN:<em>SHUGABA BUHARI YA AMINCE DA BAIWA YAN NIJERIYA RANCEN KUDADE DON MALLAKAR JIRAGEN RUWA</em>
”Pele ya gina kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashe, da ƙabilu da ma addinai, haƙiƙa duniya ba za ta manta da shi ba”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Tsohon gwarzon ɗan wasan duniyar ya mutu ne ranar alhamsi bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Ya lashe kofin duniya uku tare da zura ƙwallaye sama da 1,281, ya zama zaƙaƙurin ɗan wasan duniya.

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Ambassador Dr. Amina Umar Namadi: A First Lady Defined by Compassion, Service, and Humanity
Police Rescue Abducted Three-Day-Old Baby, Arrest Two Suspects in Nasarawa
Governor Yusuf Mourns Alhaji Nuhu Dantani
ADC Leaders Reject INEC Decision, Vow to Resist, Mobilise Support in Otukpo
Police Disburse ₦9.26m to Families of Fallen Officers in Kano