Ahmed Ado Bayero, babban hadimin hamɓararren Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya yi watsi da tsohon sarkin ya kuma yi mubaya’a ga Sarki Muhammadu Sanusi II.

Ahmad Bayero, wanda kuma shi ne Hakimin Kumbotso, ya kai ziyarar ban girma a fadar Sarki Sanusin, dake Gidan Rumfa ranar Laraba.
A cikin wani faifan bidiyo da DAILY NIGERIAN ta samu, an hango tsohon shugaban ma’aikatan, wanda ƙani ne ga hamɓararren Sarkin, ya gurfana a gaban Malam Sanusi don miƙa mubaya’ar sa.

Idan zaku tuna Gwamna Abba Yusuf ne ya naɗa Sarki Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16 a watan Mayu, bayan soke dokar Masarautar Kano ta shekarar 2019, wadda ta rusa dukkan masarautu biyar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa.
Daily Nigeria


Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Ambassador Dr. Amina Umar Namadi: A First Lady Defined by Compassion, Service, and Humanity
Police Rescue Abducted Three-Day-Old Baby, Arrest Two Suspects in Nasarawa
Governor Yusuf Mourns Alhaji Nuhu Dantani
ADC Leaders Reject INEC Decision, Vow to Resist, Mobilise Support in Otukpo
Police Disburse ₦9.26m to Families of Fallen Officers in Kano