Menu

Sha’aban Sharada ya fice daga APC, ya karbi tikitin takarar gwamna a wata jam’iyyar 

Admin 4 years ago 0

Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar birni da kewaye a jihar kano, Shaaban Ibrahim Sharada, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADP.

Bayan sauya sheka, DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa dan majalisar ya koma jam’iyyar ADP kuma ya karbi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar.

Majiya mai tushe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, ofishin INEC dake Kano, ta ce Shaaban sharada zai yiwa jam’iyyar ADP takara tare da abokin takararsa, Rabiu Bako.

Hon. Shaaban Sharada wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leken asiri, ya yi takarar neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC amma mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna ya kayar da shi.

Kadaura24 ta rawaito Dan majalisar ya kasance cikin kungiyar G-7, a jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau.

Asalin Labari… kadaura24

Leave a Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *