Daga Halliru Zaria
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kasuwa irin ta zamani da wasu ayyukan hanyoyi a kananan hukumomin Sabon Gari da zaria dake jihar kaduna.
Wakilinmu ya sami labarin cewa kasuwar zananin da aka gina a Sabon Gari tana da rumfuna 2,762 da ofishin gudanar wa da wurin ajiye motoci da ofishin Yan kwana-kwana da ofisoshin jami’an tsaro da sauran kayayyakin zamani.
Shugaban kasar ya kaddamar da kashi na daya da na biyu na kasuwar ne,ya yin da ba a kammala kashi na uku na kasuwar ba.
Ayyukan hanyoyin da aka gudanar a kananan hukumomin zaria da Sabon Gari Wanda shugaban kasar ya kaddamar na daga cikin ayyukan sabunta birane na gwamnatin jihar kaduna.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari,wanda ya sami rakiyar gwamnan jihar kaduna Nasiru Ahmed El-Rufa’i bayan sun kammala zagayen sabbin ayyukan hanyoyin a zaria sun sami tarba daga daruruwan mutane da suka fito domin yi masa maraba.
Daga bisani shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce Fadar Mai Martaba sarkin zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli domin kai masa gaisuwar ban girma,inda daga nan ya koma kaduna.
Radio Najeriya ya bada rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ziyarar aiki jihar kaduna na kwana biyu bayan ne inda kai tsaye ya sauka a kaduna daga Banjul na kasar Gambia inda aka kaddamar da Adama Barrow a matsayin shugaban kasa karo na biyu.
ASALIN LABARI RADIO NIGERIA

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Arrest of Bello Bodejo politically motivated – Campaign DG
Police Violent Crime Response Unit Records Breakthrough in Akwa Ibom Raid
2027: Church Urges Effective Deployment of Technology, Establishment of Election Offense Commission
Police, Military Recover 67 Stolen Cows, Other Livestock in Kano
Former Presidential Aide, Ja’oji, Gets House of Reps Ticket
Zamfara Police Commissioner Holds Strategic Security Meeting with Senior Officers