Uwar Gidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta ja hankalin gwamnatin Kano da ta dauki matakan kariya ga Kananan Yara don gudun kara afkuwar abin da ya faru da yarinyar nan Haneefa Abubakar da malaminta ya yiwa kisan gilla a nan Kano.
Uwar gidan shugaban kasa ta bayyana hakan ne lokacin da ta je Gidansu Iyayen Hanifa Abubakar domin yi musu ta’aziyyar Rashin ta.
Aisha Buhari ta yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa matakan data dauka tun faruwar lamarin, Sannan ta ce saurin yanke hukunci ga Waɗanda aka Samu da Wannan laifi zai kwantar da hankalin iyaye musamman mata.
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jaddadawa al’ummar Kano cewa gwamnatin Kano ba za ta kara ko minti guda ba wajen sanya hannu, Idan Kotu ta yanke hukuncin kisa akan Waɗanda ake Zargi.Uwar gidan Shugaban Kasar ta Ziyarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin yi Masa ta’aziyyar rashe-rashen da akai a Kano a yan watannin baya.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Azare Commends Peaceful Conduct of APC Primaries in Akwa Ibom
Kano South Fallout: Has Rurum Drawn a Red Line Against Kawu Sumaila?
When Ja’o’ji Answers Reconciliation With Humility in Victory
APC Aspirant Raises Concerns Over Conduct of Primary Election in Jigawa Constituency
Kano Govt Pledges Stronger Collaboration with FG, Partners on Education
Ambassador Dr Amina Umar Namadi Sponsors Mass Marriage for 300 Couples in Jigawa