Kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa ASUU a jami’ar Bayero ta ayyana ranar Litinin 7 ga Fabrairu a matsayin ranar da ba za a gudanar da karatu a jami’ar ba.
Muna nishadantuwa da Manhajar Kallo.ng – mabiya manhajar
PREMIER RADIO da ke kano ta ruwaito cewar wannan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Haruna Musa da sakatarensa Yusuf Madugu suka sanyawa hannu da yammacin ranar Alhamis.
Kungiyar ta ce a maimakon kin shiga ajin za ta yi amfani da damar wajen wayarwada kan dalibai irin halin da gwamnatin tarayya ta jefa su a ciki na kin biyansu hakkokinsu.
A cewarsu har yanzu gwamnatin tarayya ta ki cika alkawuran da ta daukarmusu duk da cewa an lallabasu aka hanasu tafiya yajin aiki.
Idan za a iya tunawa dai tun a watan Disambar bara ne kungiyar ta ASUU ta yi yunkurin tafiya yajin aiki amma aka lallabasu suka hakura, bisa alkawarin za a biya musu bukatunsu.
Sai dai a cewar kungiyar tun bayan da aka lallabasun har yanzu gwanatin taki sauraron su ballantana ta cika alkawuran da ta dauka.
A don hakan ne kungiyar taga dacewar ta tattauna da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki musamman iyayen yara wajen sanar da su halin da ake ciki.
Haka kuma tana fatan iyayen yaran da daliban ba za su zargesu ba da zarar sun yi yunkuri komawa yajin aikin.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Arrest of Bello Bodejo politically motivated – Campaign DG
Police Violent Crime Response Unit Records Breakthrough in Akwa Ibom Raid
2027: Church Urges Effective Deployment of Technology, Establishment of Election Offense Commission
Police, Military Recover 67 Stolen Cows, Other Livestock in Kano
Former Presidential Aide, Ja’oji, Gets House of Reps Ticket
Zamfara Police Commissioner Holds Strategic Security Meeting with Senior Officers