Daga Abdullahi Kano
Bayarbe na farko da ya samu muka min siyasa à jihar Kaduna, Hon. Rasheed Adekeye, ya bukaci masu ruwa da tsaki da mazauna jihar Kaduna da su marawa Dr. Bashir Jamoh baya a zaben gwamnan jihar Kaduna da ke tafe.
Hon. Adekeye ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kaduna ranar Alhamis mai taken: “Me yasa Jamoh Ya Zama Mafi alkairi ga Jihar Kaduna”.
Adekeye ya nuna jin dadinsa da cewa Jamoh zai yi daidai yadda ya kamata tare da inganta ci gaban da gwamnatin ke samu.
“Saboda haka ya zamawajibi a fadi gaskiya, gwamnatocin da suka gabata a jihar sun yi iya kokarinsu wajen ganin sun gudanar da mulki gwargwadon iyawarsu, ciki har da gwamnatin Nasir El-rufai mai ci.
“A matsayina na Bayarbe na farko da aka nada a siyasance a fagen siyasa a jihar Kaduna, kuma haifaffen jihar Kaduna kuma a nan na tashi, a gaskiya ina da yakinin cewa za a ji muryata a cikin al’amuran jihar.
“Ga wasu daga cikin mu da muka san shi, Dokta Bashir Jamoh zai yi amfani da basirarsa da fahimtar yadda ake tafiyar da fiira a cikin shugabanci.
“Sama da shekaru sama da 32 na hidimar jama’a, ya kware fasaha a cikin bangaren sufurin jiragen ruwa, Jamoh ba shi da na biyu a fannin ingancin shugabanci wanda ya gina kadarkon shugabanci na Gari a tsakanin Arewa da Kudu ,” in ji shi.
Da yake magana kan kyawawan ayyukan shugaban hukumar sufurin jiragen ruwa ta NIMASA, Adekeye ya kuma bayyana cewa Jamoh ya yi aiki a gwamnatin jihar Kaduna kafin ya mayar da aikinsa zuwa hukumar kula da jiragen ruwa ta kasa (NMA) a waccen lokacin a shekarar 1994.
A cewarsa, kafin a nada shi a matsayin shugaban NIMASA, Jamoh ya kasance babban darakta a fannin kudi da gudanarwa a NIMASA, kuma kafin nan ya kasance darakta mai ba da taimako a NIMASA mai kula da horarwa da raya kasa.
“Jamoh ya samu damar yin aiki ba kawai a fannin Gudanarwa ba, har ma a Ma’aikatun Ayyuka da Gudanarwa a cikin hukumar sufurin jiragen ruwa wanda muka san zai kawo wa wannan sabon aiki na mulkin Jihar Kaduna.
“Ci gaban basirar sa na jagoranci wanda zai zama mahimmancin Abu ga jama’a za a nuna shi a cikin kwanaki da watanni masu zuwa”, in ji shi.
Da yake magana a kan irin nasarorin da El-rufai ya samu a jihar Kaduna, Adekeye ya kuma bayyana cewa mutanen jihar da ba su daina yaba ci gaba da sabbin ayyukan da gwamnati ke samu ba, wanda a cewarsa shi ne dalilin da ya sa Dakta Bashir Jamoh ya fi kowa a jihar domin ya gaji Gwamna El-rufai.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Arrest of Bello Bodejo politically motivated – Campaign DG
Police Violent Crime Response Unit Records Breakthrough in Akwa Ibom Raid
2027: Church Urges Effective Deployment of Technology, Establishment of Election Offense Commission
Police, Military Recover 67 Stolen Cows, Other Livestock in Kano
Former Presidential Aide, Ja’oji, Gets House of Reps Ticket
Zamfara Police Commissioner Holds Strategic Security Meeting with Senior Officers