Menu

HUKUMAR NIMASA ZA TA CIGABA DA TALLAFAWA JAMI’AR SUFURIN JIRAGEN RUWA -Jamoh.

Admin 4 years ago

– Shiri ya kankama domin mayar da kwalejin ilimin kimiyya na Hukumar NIMASA dake Okoloba ya zuwa sashi na jami’ar sufurin jiragen ruwa.

– Kwararru sun iso Najeriya don samar da karamar tashar tsayawar jiragen ruwa da saukar fasinja

Babban daraktan hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, Dr. Bashir Jamoh ya jaddada kudirin hukumar na ganin jami’ar sufurin jirahen ruwa dake Okerenkoko a jihar Delta ta bunkasa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da wata tawaga daga Jami’ar ta kai ziyara ga Hukumar NIMASA da ke Legas. Ya kuma bayyana cewa duk da mika jami’ar ga Hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Hukumarsa ta himmatu wajen tallafa wa jami’ar sufurin ta NMU ta hanyar kammala ayyukan da ta fara a cikinta.

Yayin da yake ba da shawara ga hukumar Gudanarwar jami’ar da su nemi takaddun shaida na ƙasa da na duniya don tabbatar da  takaddun shaida daga makarantar sun sami karɓuwa a duniya, Jamoh ya bukaci hukumar jami’ar ta NMU da su nemi haɗin gwiwa tare da Jami’ar sufurin jiragen ruwa ta Duniya, (WMU) dama sauran cibiyoyin ilimi da suka yi fice a duniya.

“Jami’ar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya za ta iya cike gibin da ke akwai ta fuskar karancin ma’aikata a bangaren sufurin jiragen ruwa a Najeriya. Abin da ya kamata Ku yi a matsayinku na kwamitin gudanarwa shi ne neman haɗin gwiwa tare da cibiyoyi na musamman masu kamanceceniya da Ku. Kuma ku tabbatar da cewa takaddun shaida na jami’ar NMU sun dace da tsarin da aka gindiya a duniya. Burinmu shi ne mu nemo manyan ma’aikata daga NMU maimakon halin da ake ciki a yanzu inda ake fifita ma’aikatan da suka samu kwarewa daga cibiyoyin kasashen waje fiye da Najeriya.”

Shugaban NIMASA ya bayyana cewa duk da mika jami’ar ga hukumar kula da jami’o’i ta kasa, har yanzu hukumar tana tanadin kasafin kudi ga jami’ar ta NMU domin ganin an kammala ayyukan NIMASA da aka fara a jami’ar. “Mun yi imani da cewa, samar da isassun kudi ga jami’ar NMU zai inganta ayyukanta da samar da guraban Ayyuka ga matasa musamman a yankin Neja-Delta. Himmatuwarmu na samar da kudin gudanarwa ga jami’ar NMU ya dogara ne akan ƙa’idar haɓbaka kwazon aiki ga ma’aikata.” Jamoh ya CE.

Da yake tsokaci game da samar da karamar tashar tsayawa ga jirahen ruwa da saukar fasinja , shugaban NIMASA ya bayyana cewa kwararru daga masu kera jirgin ruwa sun kwashe sama da wata guda suna aiki a Najeriya suna aiki tukuru wajen Samar da tashar. Ya kuma sanar da Hukumar jami’ar ta NMU cewa wurin zai kasance don dalibai daga Jami’ar don sanin makamar aiki idan ya fara aiki.

“ Kwararru daga kamfanin da ya tashar jiragen ruwa sun dade a Najeriya, suna ba da tallafin fasaha da kuma aiki kan yadda za a tafoyar da tashar idan ta fara aiki . Lokacin da na ba su wa’adin gaggauta kammala aikin, an ba ni shawara na ƙwararru cewa kada in yi gaggawa tukuna, na bi sannu-a-hankali. Idan mun jira wannan dogon lokaci, me zai hana ba zamu iya jira yanzu ba a maimakon yin gaggawa. Dalibanmu daga wannan jami’a ta NMU da sauran cibiyoyi za a yi maraba da su don sanin makamar aiki a bangarorin injiniyoyi, lantarki, walda, da sauran wuraren idan muka fara cikakken aiki. ” Yace.

Dr Jamoh ya kuma bayyana cewa ana kan shirin mayar da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta NIMASA dake Okoloba zuwa harabar Jami’ar sufurin jirahen ruwa ta Najeriya. “Ayyukanmu na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Okoloba a Jihar Delta ba a yin amfani da su sosai. Ana ci gaba tattaunawa don mika ragamar kwalejin ya zuwa ga Hukumar Gudanarwar Jami’ar”.

A nasa bangaren, shugaban hukumar gudanarwa ta NMU wanda ya samu wakilcin Alhaji Bello Dukku Salihu ya bayyana cewa, “makarantar tana kan shirin kulla yarjejeniya da Jami’ar sufurin jiragen ruwa ta Ghana. Ya yabawa NIMASA bisa yadda take tallafa wa Jami’ar a kullum. Shi da ‘yan tawagar da suka yi magana sun nuna farin cikin su da yin karin haske game da karamar tashar tsayawa ga jiragen ruwa da saukar fasinja wanda suka yi zaton mallakin jami’ar ce.” Amma bisa karanto musu tarohin yadda taCE ihin tashar ta fara yanzu sun fahimta game da sarkakiya wannan batu cikin ruwan sanyi.