Daga Mukhtar Khalil
Mamallakin Rukunonin Kamfanin Salbas oil and gas Alhaji Sale Baba Rano, ya kudirci aniyar sayar da man fetur ba dare ba Rana har na tsahon kwanaki 7 Albarkacin Wannan wata na Ramadana Mai albarka.
Alhaji Sale Baba Rano ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Jaridar Kadaura24 a Yau labaraba .
Salbas yace ya dau wannan matakin ne, domin taimakawa al’umma su samin man a cikin yanayi Mai Sauki a kowanne lokaci Albarkacin watan Azumin Ramadan.
Haka zalika wannan mataki zai taimakawa yunkurin Kamfanin Samar da albarka man fetur na Kasa NNPC, wajen magance karancin man fetur a jihar Kano da kasa baki daya.
” Mun yi Haka ne don saukakawa al’umma, kuma Idan ka lura ana Azumin cikin rana kuma ga wahalar da man yake yi, to Amma Idan muka bada wannan Gudunmawa ta bayar da man awa 24 Ina da tabbacin al’umma zasu sami sauki”.
Salbas yace za’a bayar da man ne a Gidan Man Salbas dake kan titin BUK kusa da Kofar fanfo a birni kano a gobe alhamis 07-04-22, Inda yace an yi tanadi Jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an sami ingantaccen tsaron, yayin da ake bayar da man safe Rana da dare har na tsahon kwanaki 7.
Gidan Man dai Yana da kawuna Masu yawa Kuma akwai abubuwan more rayuwa a ciki, don tabbatar da duk Wanda ya je shan man Zai Sha ba tare da wata matsala.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito an jima ana wahalar man fetur a kasar nan, Kuma da alama da Sauran Masu gidajen Mai zasu yi koyi da Alhaji Sale Baba Rano (Salbas) da al’umma sun sami saukin wahalar man da ta Dade tana ciwa al’umma tuwo a kwarya

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Arrest of Bello Bodejo politically motivated – Campaign DG
Police Violent Crime Response Unit Records Breakthrough in Akwa Ibom Raid
2027: Church Urges Effective Deployment of Technology, Establishment of Election Offense Commission
Police, Military Recover 67 Stolen Cows, Other Livestock in Kano
Former Presidential Aide, Ja’oji, Gets House of Reps Ticket
Zamfara Police Commissioner Holds Strategic Security Meeting with Senior Officers