Daga Ammar Balarabe
Jam’iyyar ADP mai alamar littafi, ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar majalisar jiha da ta tarayya a jihar Jigawa.
Zaben ya gudana ne bisa tsarin masalaha, kamar yadda masu ruwa da tsakin jam’iyyar suka amince.
Yayin taron An amince da takarar yan majalisar jiha 30, sai na majalisar wakilai 11, da kuma na majalisar dattawa 3.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Rufa’i Bua AbdulAzeez, yace ‘’da yawun ‘ya’yan jam’iyyar aka zabi tsarin masalahar wajen fidda yan takara’’.
To sai dai, a dukkanin yan takarar da jam’iyyar ta tsayar, babu mace ko guda, wanda shugaban jam’iyyar ya alakanta da rashin shigowar matan harkokin siyasa.
‘’Ga duk yan takarar majalisar jiha 30 babu mace, haka suma yan majalisar tarayyar mu da sanatoci, babu mace.’’
‘’Alhamdulillahi, wannan abubuwa dai wanda yake a na ta wayar da kan matan amma har yanzu, kuma kofar mu a bude take, idan Allah ya kawo mana macen dake son takarar, zamu bata dama.’’ Inji Bua.
Bua AbdulAzeez ya kara da cewa ‘’Mun kawo foma foman takarar nan, inda kowanne akwai farashin da muka sanya masa, sai dai munyi rangwame wanda babu bukatar mu yayata yadda muka sayar.’’
Ya kara da cewa manufar jam’iyyarmuu idan ta sami dama itace magance manyan kalubalen da yan Najeriya ke ciki, musamman na yunwa da rashin tsaro.
‘’Babbar manufar mu shine, manyan matsalolin dake damun yan Najeriya, na yanayin wahalhalun rayuwa, rashin tsaro, mu kawo karshensu.’’
‘’Dattijan da muke tafiya tare, sun san ina aka faro kuma ina aka tsaya, a don haka zasu rika haska mana da shawarwari idan mukayin nasara.’’
A ranar Alhamis, 09 ga watan Yuni ne jam’iyyar ta ADP za kuma ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar gwamna, inda ake kyautata zaton shima masalaha za’a bi.
Da yake jawabi a wajen taron jam’iyyar, wanda ya gudana a farfajiyar gidansa dake karamar hukumar Taura, dan takarar gwamna a jam’iyyar, Alhaji Sabo Sulaiman Taura, ya bayyana gamsuwa da yadda tsarin ya gudana.
Sabo ya kuma taba alli game da kiran yayan jam’iyyar wajen kaucewa duk masu hure musu kunne da sunan jansu zuwa babbar jam’iyya.
‘’Tuni da nakeso inyi mana, kamar yadda nake fada muku a kowanne lokaci ya kamata mu jajirce. A wannan lokacin kada mu bari wani mutum yazo ya nuna mana jam’iyya ce babba, Ita ce take da Najeriya, ba ita ke da Najeriya ba kune da Najeriya, domin duk wani mutum da ka gani a wurin nan har Villa, da bazar ku yake rawa.’’
‘’Ku duba ingancin mutumin da zaku zaba, ku duba daga grassroot kusan daga ina ya fito. Ance mana jiki magayi kuma jikinmu ya gaya mana.’’
‘’Abinda nake son fada muku shine, kune gwamnati, ku zaku zabi wanda kuke so ya wakilce ku. Idan aka baku kudi, naku ne aka sata, idan kun karbe, sai ku zabi wanda ya dace.’’ Inji Alhaji Sabo Sulaiman Taura.
Taron ya sami halartar yayan jam’iyyar daga cikin da wajen jihar Jigawa, wanda a karshe aka sanar da gayyatar zuwa wajen zaben fidda gwani na yan takarar gwamna, da zai gudana a shelkwatar jam’iyyar ta jihar dake birnin Dutse.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Former Kano Federal Lawmaker Shaaban Sharada Distances Self From Barau Group’s Endorsement of New Deputy Governor
K-SAFE Hails Gov Yusuf Over ₦4.45bn Approval for Students’ Examination Fees
Governor Radda Inaugurates 2026 Hajj Committee, Charges Members on Integrity
Kenyan President Calls For Radical Overhaul Of African Union
Police Commissioner Visits Mada, Meets Stakeholders Over Rising Security Concerns in Zamfara
MALNUTRITION: Governor Radda Opens 2 Stabilization Centres, 60 OTP Sites,