Hukumar kula da harkokin iyakokin ruwa ta duniya a rahoton ta na rabin wannan shekara ta yaba da raguwar aikata laifuka a iyakokin ruwa na duniya inda ta bayyana hakan a matsayin sabon shafi ga masu mu’amala da jiragen ruwa na duniya.
A wata sanarwa da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar kula da iyakokin ruwa na kasa Mr Osagie Edward ya fitar, ya ce wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta samu rahotannin raguwar aikata laifuka na farkon wannan shekara wanda rabon da a samu irin shi tun shekarar 1994 wanda ke nuni da kokarin da hukumar ke yi wajen kara wayar da kai don kare iyakokin ruwa na duniya.

Ita dai yarjejeniyar rage aikata laifuka a gabar tekun guinea ta tabbatar da cewa ba a samu rahoton garkuwa da matafiya jirgin ruwa ba, shekara daya bayan yarjejeniyar watan Mayun shekarar 2021. Wannan cigaba ne idan aka yi la’akari da kididdigar da aka fitar a shekarar 2020 da aka yi garkuwa da matafiya jirgin ruwa kimanin mutum 130. Rahoton yarjejeniyar gabar tekun guinea ya kuma tabbatar da cewa ba a samu rahoton garkuwa don neman kudin fansa ba a wannan shekara ba kamar rahoton garkuwa na mutum ashirin ba a shekarar 2020 da kuma goma sha biyu da aka samu a shekarar 2021.
A nashi tsokacin, Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwa na kasa, Dr Bashir Jamoh yace a shirye Nijeriya take wajen bada hadin kai a nasarorin da ake samu a baya-bayan nan na a yaki da aikata laifuka a yankin. Ya kuma bayyana farin cikin shi bisa la’akari da hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya ke yi a cigaban da ake samu, wanda hakan ya biyo bayan hadin gwiwa ne tsakanin masu ruwa da tsaki na kasa, na yanki da kuma wadanda ba na yankin ba. Ya kuma bayyana fatan cewa za a cigaba a wannan tafarkin, inda ya bada tabbacin cewa ba shakka kwanan nan za a ci gajiyar wannan yarjejeniyar da ya shafi kudaden inshorar da ake biya akan jiragen dako na Nijeriya.

Da take yabawa cigaban da aka samu, majalisar mamallaka jiragen ruwa mafi girma na duniya wato BIMCO, tayi kira da a samu cikakken tsaro da kuma amfani da kadarorin deep blue sea wajen yaki da aikata laifuka akan iyakokin ruwa. Ta kuma yaba da kokarin rundunar sojin ruwan kasar nan tare da hadin gwiwar sauran rundunonin sojin ruwa na duniya wajen dakile ayyukan bata gari akan iyakokin ruwa da kuma tabbatar da bin doka da oda akan iyakokin ruwan kasar nan da kuma tarurrukan da aka yi karkashin lemar gabar tekun guinea da wayar da kan jama’a inda ta bayyana shi a matsayin jigo wajen nasarar da ake samu wajen yaki da aikata laifuka akan iyakokin ruwa a yankin.
A nata bangaren kuma, hukumar kula da kare iyakokin ruwa ta duniya ta tabbatar da cewa ba a samu rahoton sace jirgin ruwa a Nijeriya ba a farkon wannan shekarar. Ita ma kotun masu hukunta laifuka ta duniya, wato ICC da hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya-IMB sun tabbatar da cewa an samu raguwar aikata laifuka matuka akan ruwa a duniya a farkon wannan shekarar cikin shekaru 28 da suka gabata inda aka aka samu rahotanni 58 ba kamar 68 ba a wuraren shekarar 2021 ba. A cikin rahotanni 58 da aka samu kuwa, biyu daga ciki hari aka kai akan ruwa inda ba a samu ko daya akan iyakokin ruwa na Nijeriya ba. A don haka hukumomin IMB da na PRC suka bukaci da a kara zage damtse don kare kan iyakokin ruwa na duniya.
Daraktan hukumar ta IMB, Micheal Howlett yace wannan abin farin ciki ne ba ga matafiya jirgin ruwa ba, har ma da masu harkokin jirgin ruwa wanda hakan zai kara bunkasa kasuwanci da zai inganta tattalin arziki. Ya kuma bukaci masu harkokin jirgin ruwa da su lura da bangarorin da suka shafi haduran da ka iya afkuwa, sannan sukayi kira ga gwamnatoci da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki da su cigaba da sintirin su da zai zama izina ga masu aikata laifuka.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
SPMC Begins Quarterly Oversight of Project Sites, Reviews Progress Across Zone 3
NGO trains girls on reusable pads, urges parents to prioritise girl-child education
Group demands full implementation of Katsina PWDs discrimination law
Jigawa to Provide Three Daily Meals for Pilgrims in 2026 Haj
Kano Police, NEMA Strengthen Partnership on Disaster Response
Kano Police Arrest Two Over ‘Aljannu’ Phone Scam, Recover 28 SIM Cards