Menu

Jam’iyyar PDP ta sami nasara ne a jihar Osun sakamakon jajircewar matasan jam’iyyar -Shugaban Kungiyar G7 for Atiku

Admin 4 years ago

Daga Sani Danbala Gwarzo

Shugaban kungiyar G7 Business Community for Atiku Abubakar 2023 ya bayyana Nasarar jam’iyyarsu ta PDP ya samo asaline sakamakon jajirtattun matasan jam’iyyar da suka bada gudummawa mafi girma a zaben.

Ya bayyana hakane a lokacin da yake tattunawa da yan jaridu ranar lahadi a ofishinsa dake shalkwatar kungiyar dake titin gidan zoo a birnin kano. Inda ya kara da cewa “Idan alayi la’akari da adadin kason da matasa suka dauka a zaben alkaluma sun nuna matasa sun dauki akalla kaso 39.7, wanda hakan yana nuna sune sukafi bada gudummawa fiyeda kowa a zaben. Wannan kadai ya isa mahukunta su fahimci matasa sunada muhimmiyar rawar da zasu iya takawa wurin tabbatar da Nasarar jam’iyyar PDP idan har aka basu dama a cikin al’amuran zabe mai zuwa a kowane mataki.

Wannan yana daga cikin dalilan dayasa muka tsaya kai da fata akan maigirma WAZIRIN ADAMAWA saboda a cikin tsarinsa na gaba gaba wurin aiwatar da al’amuran zabe da kuma mulki akwai makomar matasa a ciki, wanda har yayi alkawarin kaso 40 cikin dari na mukamansa zai fito daga cikin matasa. Wannan shine yake kara tabbatar da ingancinsa fiyeda da duk sauran yan takarkaru na ragowar jam’iyyu”
Ya kara da cewa “Inaso na kara jan hankalin matasa yan uwana da mu kawar da lissafin jam’iyya mu fuskanci cancanta a kowane mataki, domin a halin da Nigeria take ciki duk mai hankali ba maganar jam’iyya yakeyi ba. Kowa yasan ingancin maigirma WAZIRIN ADAMAWA hatta wadanda suka wani layin sunsan yafi jagororinsu Nagarta.”


Ya kuma yabawa hukumar zabe mai zaman kanta da jami’an tsaro da suka tsaya tsayin daka wurin tabbatar da abinda al’umma suka zaba bai samu cikas ba.
A karshe ya taya Uwar jam’iyyar PDP ta kasa da dan takarar Shugabancin kasa karkashin tutar Jam’iyyar PDP da kuma zababben gwamna mai jiran rantsuwa Adeleke da daukacin yayan jam’iyyar PDP murnar nasarar da aka samu a wannan zabe, tareda fatan samun ninkin hakan a babban zabe mai zuwa.