Daga Abdullahi Kano
Rundunar Yan sandan jihar kano tayi nasarar yin awan gaba da masu laifufuka daban daban a fadin jihar cikin watanni ukku dan samar da zaman lafiya da kare rayukan al’umma da dukiyoyin su.
Tabbatar da hakan nazuwane sa’ilin da rundunar take gabatarma da manema labarai masu laifufukan a hedikwatarta bampai a jiya alhamis karkashin jagorancin mai girma kwamishinanYan sanda da akema lakabi da “NAGARI NA KOWA” watau CP Sama’ila Shu’aibu Dikko.
Ajawabinsa lokacin da yake gabatar da masu laifufukan kwamishinan ya yabama jami’an rundunar dasauran al’ummar dake taimakawa wajen bada gudunmuwar su a wannan hukumar koda yaushe.
Acikin wadanda aka kamar sunhada da Yan fashi da makami mutum 42, tareda nasarar damke mutane 9 da ake zargi da garkuwa da mutane da karbar kudin fansa,sannan rundunar ta Kama akalla mutane 16 da laifin Damfara ajahar kano.
Sauran masu laifufukan sun hada da mutane 27 da zargin laifin satar motoci da mashinan adaidaita, haka kuma akwai mutane 2 da rundunar takama da laifin safarar bil’adama, inda kuma tasamu nasarar cafke wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi su 12.
Kazalika hukumar ta samu damar kama kimanin mutane 92 da ake zargi da aikata harkar daba da Sara suka a jihar tareda kubutar da mutane 5 daga safarar su dan aikin bautarwa zuwa wasu kasashen.
Haka nan ma rundunar tasamu nasarar karbe bindigogi daban daban guda 25 da motoci guda 12 tareda mashin din adaidaita sahu guda 7 sai mashin mai kafa biyu guda 3,hakan nan ma rundunar ta karbe wukake guda 122 daga hannun masu laifi daban daban.
Sauran abubuwan da akasamu sun hada da makaman da aka hada rodi kimanin guda 96 sai parcels guda 269 da daurin tabar wiwi guda 265 da takai darajar naira milyan biyu da dubu dari bakwai da ashirin da biyar 2,725,000:00.
Sannan akwai kwamfuta laptop guda 4 da wayoyin hannu guda 134 dakuma talabijin kirar plasma guda 16, Kuma rundunar tasamu nasarar gano kwayar exol har kimanin guda 280 daga hannun wadanda ake zargi da sha da fataucin miyagun kwayoyi sai kwalaben suku daye guda 74 yayin gudanar da bincike.
Daga karshe kwamishinan yayaba da kokarin rundunar Yan sandan jihar kano da sauran bangarorin jami’an tsaro da Yan Jarida dama masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da sukeba hukumar wajen dakile bara gurbi afadin jihar kano da makwabtanta.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Bichi Moves Motion as Kano APC Stakeholders Endorse Tinubu for 2027, Raise N50m for Nomination Form
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper
Sharada Joins Kano Central Senatorial Race, Calls for Free and Fair APC Primaries
NEPC trains SMEs, MSMEs in Kano to boost export readiness
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS