Hukumar kula da iyakokin ruwa ta kasa-NIMASA ta sanya hannun a yarjejeniyar fahimtar juna da cibiyar kula da harkokin sufuri ta kasa-NITT ta fuskar bincike da horaswa don inganta tsaro akan iyakokin ruwan kasar nan.
Shugaban hukumar NIMASA, Dr Bashir Jamoh da takwaransa na NITT ne suka sa hannun da zimmar inganta kayayyakin da ake kerawa na cikin gida.
Ita da wannan yarjejeniya ta fahimta a wani bangare na nuna burin da hukumomin biyu ke da shi ne wajen ganin manyan ma’aikata a bangaren sha’anin iyakokin ruwa na samun horo na musamman a nan gida Nijeriya ba sai sun tsallaka kasashen ketare ba.
Dr Bashir Jamoh ya bayyana yarjejeniyar fahimtar junan a matsayin wacce ta ke da nufin cika babbar manufar kafa cibiyar kula da harkokin sufuri ta kasa, da kuma jaddada kudirin da hukumar NIMASA ke da shi na horas da ma’aikatan ta.
Ya kuma bayyana fatan cewa yarjejeniyar zata kyautata alaqa a tsakanin hukumomin, sannan ya bukaci cibiyar da ta cigaba da gudanar da bincike mai zurfi don bunkasa horaswa.
A nashi bangaren, Shugaban cibiyar kula da harkokin sufuri ta kasa, Dr Bayero Salih Farah ya bayyana godiyar shine ga hukumar NIMASA bisa ga gudunmawar da take baiwa cibiyar ta fuskar tallafin kudi na kai tsaye da kuma bada daman horas da ma’aikatan ta NIMASA shekara da shekaru.
Ya kuma sha alwashin cewa cibiyar za tayi aiki tare da NIMASA da kuma tabbatar da cewa cibiyar tana bada horaswa da gudanar da bincike-bincike daidai da na zamani.
Dr Bayero Salih Farah yace cibiyar na horas da ma’aikata da ke aiki a bangaren sufuri inda take bada shaidar takardun diploma, babbar diploma, da ta shaidar digiri na biyu a sha’anin sufuri.
A daya bangaren kuma NIMASA na cigaba da rungumar horas da ma’aikatanta don inganta kula da iyakokin ruwan Nijeriya da kuma hada gwiwa da ma’aikatu da dama don samar da tsaro a kan iyakokin na ruwa.


Naja’atu Muhammad; Pantami nada Suffar Munafikai
Zaben Gwamna A Gombe: Dalilan da Ya Sa Sardaunan Gombe Ya Zama Mafi Sauƙin Ɗan Takarar Gwamna da Za a Gabatar wa Jama’a
Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano .
Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
Kano Police Arrest 244 Suspects, Recover Guns, Drugs, 17 Vehicles
Kano Hajj: Pilgrims Board gives intending pilgrims Sept. 5 passport deadline
MPPPME Submits Key Achievements, Proposed Legacy Projects for 2027 AKY Blueprint
Customs Sharpens Operational Edge as 50 Officers Graduate from NCCSC Gwagwalada
Abbas Distributes 500 Motorcycles to Teachers in Zaria
The Political Vision of Hon Fatima Bintu Ahmad