Masarautar Erunmu Owu dake Abeokuta a Jihar Ogun taga zabi Hajiya Fanna Muhd Kawu, ta bata Sarautar Yaye Akinrunwa, domin kara samar da hadin kai tsakanin Yan Arewa da kudancin Najeriya.
Cheif Hajiya Fanna, ta kasance Mai taimako da jikan Al’umma batare da nuna bambanci ba, Kuma tana kan gaba wajen sanin magungunan gargajiya dana addinin Islama.
Cheif Hajiya Fanna Muhd, ta samu nasarar tsallake dukkan matakan da ake bukata a Masarautar Erunmu kafin baiwa kowane mutum sarauta.
A ranar 17 ga watan Satumbar shekarar 2022, Oluroko Abdul Waheed Ayoade , wato Oluroko na Masarautar Erunmu Owu ya nada Chief Hajiya Fanna Muhd Kawu, Sarautar “YeYe Akinrunwa,” Adaidai lokacin da Sarkin yake murnar cikarsa Shekara daya akan karagar mulki.
Dimbin Al’umma dake ciki da wajen Jihar Ogun suma halarci taron nadin Chief Fanna Muhd Kawu wannnan mukami, sannan ita kanta ta tafi da mutane 10.
Tawagar Sarkin Shareefai dake Legas da Ogun da Yan majalisarsu suka halarci taron wanda dimbin al’ummar Masarautar suka cika da murna ganin cewa Hajiya Fanna itace mace ta farko daga Arewacin Najeriya da aka taba baiwa Sarauta a Masarautar Erunmu Owu, kuma sarautace da suka bayyanata a matsayin macen da zata kawowa Masarautar alheri da cigaba.
Sarkin Masarautar Erunmu Owu, Oluroko Abdul Waheed Ayoade, yace Cheif Hajiya Fanna tana da nagarta wadda ta dace a bata wannnan sarauta, kuma tana da kwazo da tausayi da hidima ga Al’umma sannnan tana da ilimi da sani akan abubuawa irir iri.
Yace wadannan suna daga cikin kyawawan halayen da suka sanya Yan Majalisar Masarautar Erunmu Owu suka amince a bata wannnan sarauta, cikin wadanda suka yarda akwai Tsohon Shugaban Najeriya Cheif Olusegun Obasanjo GCFR da masu zaben Sarki su 8
wannnan biki ya Sanya Jama’a farinciki sabo da yadda Cheif Hajiya Fanna ta rika kokarin kyautatawa Mahalarta taron masu dimbin yawa.
‘Yan uwa da abokan arziki suka cigaba da Taya Cheif Fanna Muhd, samun wannnan sarauta mai girma da daraja.
Kazalika itace Sarkin yakin Magani magani ta Jihar Kano Kuma Sarauniyar Shareefan Najeriya

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Bichi Moves Motion as Kano APC Stakeholders Endorse Tinubu for 2027, Raise N50m for Nomination Form
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper
Sharada Joins Kano Central Senatorial Race, Calls for Free and Fair APC Primaries
NEPC trains SMEs, MSMEs in Kano to boost export readiness
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS