Maimartaba Sarkin Kano na goma sha hudu kuma Khalifan Tijjaniyya a Najeriya ya caccaki matakin gwamnatin Najeriya na hana shigowa da abinci kasar yana mai cewa mataki ne da ba zai haifar wa Najeriya d’a mai ido ba.
Tsohon Sarkin na Kano wanda masanin tattalin arziki ne kuma tsohon gwamnan babban bankin kasa ne “CBN” ya ce hana shigowa da abinci ba zai ta’ba maganin koma bayan tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta ba.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Tsohon Sarkin ya yi wannan jawabi ne a matsayin bako na musamman a wani taron jama’a da aka gabatar a karshen mako.
“Rashin samar da kayyayakin gida masu muhimmanci shi ne abin da ya kamata a magance tare da canjin manufofin da za su fitar da kasar ga gaci da kuma ci gaba a samar da kayyayaki na gida ba wai dakatar da shigo da abinci ba.” A cewar Tsohon Sarkin Kano Sunusi
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta yanke shawarar tattalin arzikin da take so ta gudanar.
Tun hawan Buhari mulki al’umma ke kokawa da yunwa gami da tsadar rayuwa musamman hauhawar farashi, wanda masana suka ce matakan gwamnatin Buhari ne suka sabbaba. Tuni al’ummar Najeriya suka dora laifin halin da tattalin arzikin da kasar ke ciki a kan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa ba su taba riskar irin wannan ba kafin zuwan Buharin.
asalin labari jaridar Rariya

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy
Group Endorses Senator Barau for 2027, Cites Development Record in Kano North
How AA Zaura escaped mob attack by miscreant at Farm centre