Menu

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.

Admin 3 hours ago

A wani ra’ayin Jama’a da Jaridar abknews24 taji a sassa daban daban na Kanana Hukumomin Jihar Kano 44 a cikin mako guda, Kashi 89.7% sun Zabi Murtala Sule Garo a Matsayin Wanda zai yiwa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Mataimakin.

Tun dai bayan da aka Sami gurbin Mataimakin Gwamnan Kano mabukata kujerar Mataimakin Gwamnan suke ta hankoron Yadda zasu daman kasancewa a wannan matsayin.

Idan akayi duba nabtsanaki a duk cikin manema wannan kujera ta matsaimakin Gwamnan babu Dan Siyasar da yakai gogewa irin ta Murtala Sule Garo bisa wasu dalilai.

Wadanda suka hada da kasancewarsa Dan Siyasar da ya fara tun daga Tushe wato mazaba har yakai ga mata kin da yake a yanzu.

Garo ya rike mukamai daban daban a matakin Gwamnati da Jam’iyya, bayan wasu kwamitoci da ya jagoranta har yakai ga matakin nasara.

Ya kasance Mutum ne na kowa da yake taimako Dan Jam’iyarsa da Wanda ma ba Jam’iyar su daya ba domin karamci irin nasa.

A shiyasan ce babu Wanda ya cancanta Zama wannan matsayi na Mataimakin Gwamnan Jihar Kano a yanzu domin tafiya da Yan Siyasa dai dai da zamani kamar Murtala Sule Garo.

A karshen binciken wannan jari dar dai ta kammala shi da cewa samun Nasarar Jam’iyar APC a Jihar Kano da Kasa baki daya Sai da saka hannun Murtala Sule Garo.

Duk da irin wannan nagarta ta Murtala Sule Garo Amma wasu ke kokarin cin dunduniyarsa kamar yadda mukaji daga bakin wasu da muka tattauna dasu.