Menu

BABBAN SAKATAREN HUKUMAR KULA DA IYAKOKIN RUWA NA DUNIYA YA JINJINAWA HUKUMAR NIMASA

Admin 4 years ago

Babban Sakataren kula da iyakokin ruwa na duniya, Mr Kitack Lim ya jinjinawa hukumar NIMASA da na rundunar sojin ruwan kasar nan bisa ga hadin gwiwar su da sauran abokan hulda na kasashen ketare wajen yaki da aikata laifuka akan iyakokin ruwan kasar nan.

Mr Kitack Lim yayi wannan yabon ne a wajen taron karawa juna sani akan iyakokin ruwa wanda ke ci a halin yanzu a birnin Ikko.

KARANTA WANNAN MA:AN YABAWA HUKUMAR NIMASA BISA TAFIYA DA MATA

A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar ta NIMASA Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai, yace babban sakataren ya bada tabbacin cewa kungiyar za ta cigaba da goyon bayan Nijeriya a kokarin ta na samar da tsaftacaccen teku da inganta hada-hadar sufurin jiragen ruwa.

Ya kuma bukacin yin hadin gwiwa wajen samar da tashan jiragen ruwa daya tilo ga Afrika maso yamma da kuma Afrika ta tsakiya.

Mr Lim ya kuma kawo shawarar karawa mata guraben ayyuka a bangaren iyakokin ruwan kasar nan, inda yayi nuni da cewa a saboda haka ne ake sa ran yin bikin ranar mata masu aiki a bangaren iyakokin ruwa na duniya a shekara mai kamawa.