Menu

Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan

Admin 5 months ago

 

Usman Ahmed, kaduna.

Manoma da dama sun kuka GA Gwamnati Tarayya da tayi dukkan abinda ya dace Don Ganin an Samu Dai Dai tuwa, tskanin farashin Abinci, Taki da Kuma sauran Kayan noma.

Ayayin taron shekara shekara Wanda Babba Maikatar Aikin Gona da samar da Abinci, Karo na 47th dake gudana a kaduna, (National council on agriculture and food security, Wanda babban sakataren dindindin na ma’aikatar gona yayi jawabi, Dr Marcus Ogunbiyi, na nuni da cewa Gwamnati Tarayya a shirye take da Karbar shawarwari daga dukkan bangarori Don cikagaban kasar nan.

Honourable Iliyasu Aliyu Gitel, Kwamishin Mai’aikatar Noma ta jihar Bauchi, a yayin tattaunawa da yanjarida, Bayan yabo, yaja hankalin Gwamnati Tarayya datayi kokari yadda, Manoma da talakawa zasu amfana.
Kwamishinan yayi bayyana irin kokarin da Gwamnati Bauchi key karkashin, Gwamna, Mai Girman, Bala Muhammad, kauran Bauchi keyi Don Jin dadin jama’a.

Yayi jawabi da Mai tsawo yadda Gwamnatin Bauchi ke temakawa Manoma da sauran jama’a ta hanyoyi da dama, Taki, Kayan noma, tractoci, inganta hanyoyi da dai sauransu.

 

Awata zantawa da Alhaji Sadisu Ibrahim, Shugaban kungiyar manoma matsakaita, ( National Fruits and Vegetables production and marketers cooperative federation ltd), acewar sa, Taki baya tabuwa, manoma suna asara da dama, ya wajaba Gwamnati ta yi dukkan yadda yakamata, Manoma na bukatar tallafi da bashi Don cigaban kasa. Yayi Kira ga maharta taron dasu tattauna yadda yakamata, a fidda tsari mai kyau