Menu

TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA

Admin 4 months ago

 

Kungiyar Cigaban Al’ummar Anguwan Kakaki (KPA), Karkashin jogoran Alh. Amin Mahmood da hadin gwaiwar Asibitin Koyarwa na Dabbobi dake Karkashin Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ta shirta bita don horar da matasa da Mata na kwana daya Kan dubarun kiwon kaji da Kifi.

Da yake gabatar da makala ta farko a Kan kiwon Kaji Professor Lawal Sa’idu daga Asibitin Koyarwa na kiwon dabbobi na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, yayi jawabi Mai tsawo Kan sabbin dubarun kiwon kaji musamman masu Samar da nama, daku yanda zaa rage yawan mutuwar wadannan Kaji lokacin kiwonsu don samun riba Mai yawa.

Shima anasa Jawabin Mai gabatar da kasida ta biyu akan kiwon kifi, Wanda kuma shine Shugaban wannan Kungiyar ta Cigaban Al’ummar Kakaki Alh. Amin Mahmood, ya dauki lokaci ma tsawo don fayyace Yadda zaa dunkari kiwon kifi tsakanin matasa da Mata, da kuma nuna irin alherin da Ake samu cikin wannan kiwo.

Daga bisani yaja hankalin matasa dasu dage wajen gannin sun rungumi wannan taginashi da Uwar Kungiyar Cigaban Al’ummar Kakaki ke bayar lokaci bayan lokaci.

Tunda farko Shugaban Kwamitin dattijan Anguwan Kakaki Alh. Hassan Dalhatu (Cigarin Zazzau), Wanda yasami wakilcin Alh. Jafaru Suleiman ya godewa daukacin shuwagabannin wannan Kungiya ganin Yadda suka dukufa wajen bada tallafi tare da horaswa ga matasa don ganin sun dogara da Kansu.

Itama Shugabar Kungiyar Mata Manoma ta Nigeria reshen karamar hukumar Zaria Hajia Aisha Muhammad ta godewa wannan Kungiya saboda hangen nesanta na shirya wannan horo don ganin Mata da matasa sun tsaya da kafafunsu.

Shugabar tace yadace a Samar da wata hanya da zasu rinka samun irin kifi a saukake don kiwo, da kuma kafa gidauniyar tallafawa juna tsakanin Mata manoma da Kungiyar KPA.

A jawabinsa na godiya maitainakin Shugaban Kungiyar Cigaban Al’ummar Kakaki Alhaji Alhassan Nuhu ya nuna farin ciki mara misaltuwa da murna da irin wadannan bita da Ake kokarin shiryawa don ganin matasan wannan Anguwa sun Zama abin koyi, kana yayi addaur Allah ya maida kowa gida lafiya Amin.