TATTAUNAWA
Ganin yarda ake cigaba da kuskantar matsalar tsaro a Sassa daban – dabam a kasar nan, Kuma zaben shakara ta 2023 ke sanyo Kai ,haka Kuma ana ta samun kiraye- kirayen cewar mulki kasan nan a shakara ta 2023 daya koma Kudanci kasar nan, daga Kungiyoyi da ban dabam na Matasa daga Arewaci dama Kudancin Kasa , tare Kuma da ambatar Sunayen wasu da su fito don yin Takarar Shugabancin kasar, wan nan kasa,
Wan nan yasa na tatauna da Shugaban gamayyar Kungiyoyin Matasan arewacin Najeriya wato Nastura Ashir Sharif, wanda har’ila yau shine Kuma Shugaban Matasa na Kungiyar Tuntuba ta Arewa wato( ACF) a takaice don sanin ko ya suke kallon makomar kasar tare Kuma da sanin kowaye dan takarar su a zabe mai zuwa na 2023 dama sauran batutuwa a Tattaunawarsu a Kaduna,
Ga dai yarda Tattaunawarsa ta guda na da wakilin mu a Kaduna ABDULLAHI ALHASSAN.
Wakilin Mu : koya kuke kallon makomar kasar nan……..?
Nastura Ashir Sharif. Wato Al’muran suna da dimautuwa wato dimau ta dan Adam duk tunaninsa da Kuma fargaba acikin yarda ake kallon makomar kasar sakamakon abubuwa Kamar guda biyar,
Na farko matsalar ta rashin tsoro datake cigaba,
Na biyu rushewar tattalin arzikin kasa na Uku talauci da kullum yake da -da karuwa ,Mutane suna rasa Jarikansu sakamakon tsadar rayuwa aksar akwai magana ta hauhawar farashi na kayan amfanin na kasa sanan ga Shugabanci mara nagarta mara Kyau,
To duk inda aka samu wayan nan abubuwa hakika dole duk wani dan kasa hankalin sa ya tashi domin yasan makamar kasar tana cikin hatsari,ga rashin aiyukanyi na Matasa ko kayi makaranta ko bakayi ba ,
To wayan nan duka wato alkalima ne suke nuna cewar kwantacceyar fitina a cikin kasa,indai akwai wayan nan abubuwa to sai dai fatammu ubangiji Allah ya kawo wa kasan mafita, Kuma ya ubangiji Allah ya kawo Mata Shugaban ni nagari domin ldan ansamu Shugaban ni nagari wayan da zasu lya rike amana kasa su tabbatar wayanda suke Ma’aikata dana kasa dasu basuyi amfani da wata dama ba suna satar kudaden kasa ba ,zuwa inda akasa abin ya je musu to in ansamu Shugaban ni wanda zasu tasaya kan wan nen abubuwa to insha Allahu kasar nan zata samu makoma tagari Kuma muna fatan samun haka , Shugaban nin da zasu jajirce kan gyaran wan Al’muran.
Wakilin Mu:To ko waye dan takarar ku a zabe mai zuwa2023 ..?
Nastura Ashir Sharif:To mu a kungiyance bamu da dan takara, amma dan takarar mu shine Shugaba wanda yake adali mai gaskiya wanda yake zai lya rike Mutanen kasa nan ya yaki wayen nan munannan aiyuka da suke faruwa acikin kasa wan nan shine mukeso,
Kuma duk Shugaban da zai lya bada wan Jagoranci nagari ya zauna ya rike Mutanen tsakani da Allah babu kabilanci babu almundahana ba yaudara babu karya to mu ko a lna yake maraba dashi in dai zai zauna ya yi tsakanin sa da Allah ya taimaki Mutane ya kawo karshen rashin tsaro nan ,a tursassa a toshe duk hanyoyi da Ma’aikata da wasu yan Siyasa suke hada kai suke kwashe kudaden kasa suna barin Mutanen kasa cikin rigima ta talauci da tashin hankali,
to mu ko waye wan nan shine dan takarar mu.
Shugaba Buhari ya ceto kasar nan daga durkushewa -Malami
Kuma bawai Shugaban kasa kawai muke magana ba, muna magana kan ko wani ofis da za’a zabe Mutane su tsaya su zabe Mutane Sahihahu ba Mutane dasu zo su baka magi, ko gishiri, ko omo,ko awara,ko wani dan Kudin da ba zai lsheka cefanen rana guda ba ,aje a basu kuri’a ba, ba irin wayan nan Mutanen ba ,
Mu tunanin mu a samu Mutane Sahihai kuma nagartattu Kuma lafiyaryu ba irin Mutanen da shekaru suka janye mu su ba sun shiga halin dimuwa suna neman Mutumin da zai taimaka musu har zuwa karshen rayuwarsu ,ace Kuma a dauko su a dora musu nauyi dawainiyar al’umma ba,mu bama goyon bayan irin wan nan Mutane ,masu irin wan nan shekaru,
Muna so a samo Mutane ingantattu lafiyaryu wanda kwakwalwarsu take tafiya tana yin aikin da ya kamata Kuma jikinsu zai lya daukar dawainiyar sa hankalinsu ba wanda kurin zai dauki mulki ya bar yara kanana suje suna sha’aninsu ko Kuma wasu Mutane da suke kusa dashi ko yan barandarsa saboda shi ya riga ya tsufa takansa kawai yake yi a nemi Shugabanni to ko lna aka duba suna da gogewa da cencenta da lafiya da lokaci da zasu lya bayarwa a gyara kasa da gina kasa mu shine dan takarar mu,
Ba kawai Shugaban kasa muna so harda Sauran mukamai Kamar,Sanatoci,yan Majalisar Tarayya da na Jihohi da ma sauran duk muka man wan dan Yan shine irin Mutanen da muka so a Shugabanci.
Wakilin Mu :Ganin cewar ana ta kiraye- kirayen daga Kungiyoyin Matasa Kasar nan kudunci dama Arewaci na cewar wasu fito don tsayawa takara?
Nastura Ashir Sharif:To ai kasan lokacine na zabe saboda haka da dillalan Mutane dana Siyasa duk fitowa suke suna baje kolin su, Kuma akwai Mutanen da komai lalacewar Mutum haka zasu yi mai talla babu abinda ya dame su ,ln dai zaka basu kudi baruwansu da lalacewar sa , bukatar al’umma su, su dai kansu kawai suka sani,
Sobada haka Mutane su gane cewar fa yanzu bada bane da za’a chausa musu gurbatattatun Mutane saboda bukatar wasu, su bude lda nunsu su zabi Mutane Jajirtatatu wandan da zasu kula da bukata tunsu da Kuma damuwar su, amma masu kiraye – kiraye baka lya hana su ba , amma laile Mutane su tsaya su zabi Mutane Jajirtatatu masu Mutunci da Kuma wanda zasu kula da damuwar don kada a koma gidan jiya ,wan nan shine Matsayar mu.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy
Group Endorses Senator Barau for 2027, Cites Development Record in Kano North
How AA Zaura escaped mob attack by miscreant at Farm centre