Daga Halliru Zaria
Mai Alfarma Sarkin musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayyana ilimi a matsayin hanyar magance matsalar tsaron da ta addabi Kasar nan.
Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wurin bukin yaye dalibai da cika shekara ashirin da biyar da kafa makarantar Nurul Tilawah dake Zaria.
Mai Alfarma Sarkin musulmin,wanda ya danganta yawaitar aikata miyagun ayyuka da rashin tsaro musamman a yankin Arewa akan rashin ingantaccen ilimi,ya ce idan gwamnati da al’umma suka baiwa matasa ingantaccen ilimi babu shakka matsalar za ta kau.
Mai Alfarma Muhammadu Sa’ad ya taya daliban da aka yaye murnar haddace Alkur’ani Mai tsarki a cikin shekara daya,ya kuma bukace su da su yi amfani da ilimin da ilimin da suka samu wajen magance rashin ya kamata a tsakanin Yan uwan su matasa domin wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Da yake jawabi tunda farko, shugaban makarantar,Hafiz Nura Umar Tahir ya ce dalibai sittin da biyu daga kasashen Afrika daban-daban da nahiyar turai ne suka kammala makarantar bayan sun haddace Alkur’ani cikin shekara daya.
Hafiz Tahir ya bayyana cewa daga cikin daliban akwai wata yarinya Mai shekaru 14 Yar kasar Faransa da ta haddace Alkur’anin cikin watanni 4,inda ya bayyana cewa ba su taba samun haka ba.
Manyan baki da dama ne suka halarci bukin da suka hada da sarakunan Zazzau da Kano da Zamfaran Anka da Funakaye da wakilai daga kasashen Turkiya da masar.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper
Sharada Joins Kano Central Senatorial Race, Calls for Free and Fair APC Primaries
NEPC trains SMEs, MSMEs in Kano to boost export readiness
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists