Menu

Majalisar karamar hukumar Rano ta Kaddamar da aikin samar da hasken wutar lantarki a unguwar dam dake cikin gari Rano.

Admin 4 years ago

Daga Faragai


Shugaban karamar hukumar Alhaji Dahiru Muhammed Ruwan Kanya ne ya sanar da hakan a lokacin da yake bikin kaddamar da aikin kwangilar.
Jamiin shiyar yada labarai na Rano Nasiru Habu Faragai ya shaida mana cewa, shugaban karamar hukumar Alhaji Dahiru Muhammed Ruwan Kanya, ya bayyana cewa aikin samar da wutar lantarkin a unguwar dam din zai lashe kudi naira miliyan takwas, za kuma a kammala shi cikin watanni uku kacal.
Alhaji Dahiru Ruwan Kanya yace duba da tsawon lokacin da al’ummar wannan unguwa suka shafe cikin duhu, yasa
majalisar sa ta yanke shawarar samar musu da wutar lantarkin domin bunkasa tattalin arzikinsu dama cigaba Mai dorewa.
Anasa Jawabin, Dan kwangilar da zai gudanar da aikin, injiniya Ado Baffa, alkawari yayi na kammala aikin cikin sati uku maimakon watanni uku da aka cimma yarjejeniyar. Ya kuma yi alkawari gudanar da aiki Mai inganci.
Anasu jawaban, wasu mazauna yankin, sun yabawa majalisar karamar hukumar ta Rano bisa kawo musu dauki.
A wani labarin kuma, shugaban karamar hukumàr ya bude makarantar Islamiyar garin Zambur dake mazabar Zurgu Wanda Karamar hukumar ta gyara, ya kuma yi must fatan duba yadda zaa gyara hanyar motar su daga Rano zuwa garin na Zamb ur.
Ya kuma yi Kira ga iyayen yara dake yankin su Sanya yaransu a makarantun islamiya dana zamani domin samun rayuwà ta gari a nan gaba.
Haka kuma shugaban karamar hukumar ya karbi ba kuncin al’ummar garin Jan garu dake mazabar Saji, Wanda suka kawo Mai ziyarar godiya bisa Samar musu da masallacin hams asalawatu a garin nasu.
Daga nan shugaban karamar hukumar yayi amfani da wannan dama Inda yayi Kira ga wadanda shekarunsu na haihuwa ya Kai 18 dasuyi rijistar zabe ko kuma su Sanbuta wacce suke da ita bisa mahimancinta.