Menu

NIMASA TA SAMU SABON KWAMANDAN KULA DA RUWAYEN KASAR NAN

Admin 4 years ago

Daga Adnan Abdullahi

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta nada Commodore Aliyu Gaya a matsayin sabon kwamandan da ke tsaron teku na hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA. Commodore Aliyu Gaya ya maye gurbin Commodore Ezekiel Nyako Lamiri, wanda aka mayar da shi makarantar horas da sojoji ta Najeriya.

Har zuwa lokacin da aka nada shi, Commodore Gaya shi ne Daraktan rundunar hafaka ta kasashen yammacin Afrika ECOWAS dake sa ido kan ruwaye dake yankin na shiyyar Zone E dake Cotonou a jumhuriya Benin. Ya rike wasu mukamai na soja da kwamanda a cikin wasu rundunoni na sojojin ruwa daban-daban a ciki da wajen kasar nan.

Commodore Gaya ya yi digirin farko na Kimiyya a Chemistry da Digiri na biyu a Defence Management Command and Strategy. Har ila yau, yana da takardar shaida da ya samu a Cibiyar Koyar da Zaman Lafiya ta Duniya ta Koffi Annan dake Accra, Ghana.

Takarar Gwamnan Kaduna a 2023: Shugaban matasan Yarbawa ya bayyana halayen Dr. Jamoh

Ita dai rundunar dake samar sa tsaro kan ruwayen kasar nan ta samo asali ne daga Yarjejeniyar Fahimta da aka kulla tsakanin NIMASA da Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya don inganta dangantakar aiki ta kud da kut tsakanin sassan biyu na gwamnati wajen tabbatar da tsaron yankin tekun Najeriya.

Darakta Janar na NIMASA, Dr Bashir Jamoh, ya jaddada kudirin hukumar na ci gaba da yin hadin gwiwa da sojojin ruwa na Najeriya da sauran rundunonin sojin Najeriya domin tabbatar da tsaron iyakokin kasar da ma gabar tekun Guinea.

Dr Jamoh ya ce, “Hukumar a don haka ta yabawa Rundunar Ruwan Najeriya saboda mutunta wannan yarjejeniya na tura ƙwararrun jami’ai a koyaushe zuwa Hukumar Tsaron ruwa ta NIMASA tare da tabbatar da ingantaccen iyakokin ruwa don amfanin ƙasa da al’ummomin duniya.