Tabbatuwar Tsaro a Tekun Guinea shine abin da muka fi maida hankali a kai – Jamoh
Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA a matsayinta na ja gaba a karkashin ma’aikatar sufuri da kuma rundunar sojojin ruwa ta Najeriya tare da hadin gwiwar cibiyar hadin gwiwa tsakanin yankuna na ICC dake Yaoundé, sun kammala shirye-shiryen karbar bakuncin babban taro karo na biyar na hadin gwiwa domin sa ido kan tsaro a gabar tekun Guinea da manufar karawa juna sani da kuma rage rigingimu da ake samu.
Babban Taron wanda zai gudana a babban birnin tarayya Abuja daga ranar 10 zuwa 11 ga watan Mayu an yi masa lakabi da “Samar da Tsaro mai Dorewa”, India ake sa ran dukkan sojojin ruwa na yankin da sauran masu ruwa da tsaki na duniya za su halarta.
Da yake jawabi gabanin taron, babban daraktan hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, Dr. Bashir Jamoh, ya bayyana hadin gwiwar yankin a matsayin muhimmiyar rawa wajen rage matsalar fashin teku a mashigin tekun Guinea.
A cewarsa, shirya taron zai baiwa masu ruwa da tsaki a yankin gabar tekun Guinea dama wajen yankin damar yin cudanya da tattaunawa kan yadda za a magance matsalar fashin teku a yankin. Mun yi imanin cewa hakan ya kasance sanadin rashin tsaro. -Masu ruwa da tsaki na yankin su tashi tsaye wajen fara gudanar da ayyukan tabbatar da doka a cikin teku don tallafawa kokarin da ake yi a yankin”. “Wadannan tsare-tsare na hadin gwiwa da kokarin da sojojin ruwan Najeriya da sauran sojojin ruwa na yankin suka yi ciki har da fara aiwatar da shirin samar da tsaro a teku na Deep Blue Project, shi ne ya yi silar rage yawaitar ayyukan fashin teku a ruwan Najeriya da yankin gabar Guinea. Abin lura da jin dadi shi ne hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta kasa da kasa-IMB ta cire sunab Najeriya daga jerin kasashen sake fama da matsalar fashion teku, samun wannan nasara ba abu ne mai sauki ba, amma dorewar wannan matsayi zai fi zama kalubale.
Najeriya da kasashe 22 mambobib ICC ne suka kafa dandalin hadin gwiwar Gulf of Guinea Forum SHDE a watan Yulin 2021. Manufar ita ce aiwatar da ingantaccen hadin gwiwar yaki da fashin teku a tsakanin sojojin ruwa na yankin da na kasa da kasa da kuma masana’antar jigilar kayayyaki da Cibiyoyin bayar da rahoto na Yaounde don Tsarin inganta Tsaro kan sufurin jiragen ruwa a Tsakiyar Afrika da Yammacin Afirka.
Babban taron da ya gabata wanda aka gudanar kusan a watan Yulin bara, saboda hana tafiye-tafiye da cutar ta Covid-19 ta kawo, kuma Cibiyar Kula da Maritime ta Gulf of Guinea (GOGMI) ta shirya a Accra, Ghana.
Mai girma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Karamin Ministan Sufuri, Sanata Gbemisola Saraki, Shugaban Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral AZ Gambo da Shugaban Hukumar NIMASA, Dr Bashir Jamoh ne ake sa ran zasu halarci taron daga Najeriya, yayin da Captain Bell Bell na cibiya ICC dake Yaounde shi zai jagoranci sojojin ruwa na duniya da sauran mahalarta taron.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy
Group Endorses Senator Barau for 2027, Cites Development Record in Kano North
How AA Zaura escaped mob attack by miscreant at Farm centre