Menu

TARIHIN MARIGAYI ALKALI NUHU MUSTAFA ZARIYA

Admin 4 years ago

.

Marigayi Alkalin Alkalai. Alh. Nuhu Mustafa Albarkawa.Cikin Birnin Zariya.

Marigayi Alkali Nuhu Mustafa ya Fara aikin ne a Lokacin Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau.Alhaji Muhammadu Aminu. A Lokacin da ya Nadashi Alkalin Alkalai Grand Khadi, A Lokacin Sarakuna ke Nada Alkalai, Wanda Suke Gudanar da Shari’a a Fadan Sarki.

Bayan Rushen Wannan tsari. An kara Samar da kotunan Shari’a. A Lokacin da Jahar kaduna da Jahar katsina, suke hade. Marigayi Alkali Nuhu Mustafa, ya Zama alkali Mai kula da Yan kunan Dutsanma, da Makarfi, Da Manunfashi, da Wasu Garuruwa. A Wancen Lokaci. A Karshe Marigayi Alkali Nuhu Mustafa, Yayi Ritayarsa a Garin Zariya. Bayan Kammala wa’adin aikinsa.

Mai Girma alkali Nuhu Mustafa Allah Yayi mishi Rasuwa a Shekaran 1987. Ya Rasu yabar Matan Aure da ‘ya’ya Maza da Mata. A Cikin ‘ya’yansa da yabari a kwai Wanda Yagajeshi a Fannin aikin Shari’a. Shine. Malam Sulaiman Nuhu Zaria. Sai Alhaji Mustapha Jumare. Darakta a Fannin kiwon Lafiya na Jahar kaduna. Director Nursing Services Kaduna State. Sai Kuma Alhaji Alhassan Nuhu Mustafa. Director Planning Unit NEMA. Sai Kuma Alhaji Ahmed Nuhu Mustafa. Librarian A Jami’ar Usman Danfodiyo Dake Jahar Sakoto.

Muna Addu’ar Allah Ya Gafarta Mashi. Allah ya Jaddada Rahama Agareshi, Tare da Magabatanmu. Amin

@zagezagiayau

16July2022