Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan-NIMASA ta bada gudunmawar kayayyakin kula da lafiya a wasu asibitoci da ke yankin babban birnin tarayya, Abuja.
Wannan na kunshe ne a sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin ikko.
Da yake gabatar da kayayyakin, Shugaban hukumar, Dr Bashir Yusuf Jamoh wanda Daraktan ayyuka na musamman a hukumar Mr Isichei Osamgbi ya wakilta, yayi bayanin cewa gudunmawar wata dama ce na kyautata dangantaka tsakanin hukumar da sauran hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da kuma daidaikun jama’a.
Shugaban hukumar ya kara da cewa baya ga asibitin yankin Asokoro da ya amfana da wannan gudunmawa, ana sa ran sauran asibitocin da ke yankin na babban birnin tarayya su ma za su amfana.
Dr Bashir Jamoh har ila yau yayi nuni da cewa wannan gudunmawa na da nufin tallafawa kokarin gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki wajen inganta kiwon lafiya a fadin kasar nan.

Tunda farko a jawabin shi, babban sakatare a hukumar bada agajin gaggawa na birnin tarayya, kuma shugaban asibitin yankin Asokoro, Alhaji Abbas Idris ya bayyana godiyar shi ne ga hukumar ta NIMASA bisa wannan gudunmawar, yana mai nuni da cewa kayayyakin za su taimaka wajen inganta lafiya a yankin na babban birnin tarayya.
Kawo yanzu dai, hukumar NIMASA ta bada gudunmawar kula da lafiya, kayayyakin karatu, kayayyakin inganta tsaro da kuma kayayyakin rage radadi a jihohi daban-daban dake fadin kasar nan.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper
Sharada Joins Kano Central Senatorial Race, Calls for Free and Fair APC Primaries
NEPC trains SMEs, MSMEs in Kano to boost export readiness
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists