Menu

Zamu Bunkasa Ayyukan Tashar Tsandauri da ke Garin Onne a jihar Rivers – Ministan Sufuri

Admin 4 years ago

Gwamnatin tarraya ta nanata kudurinta wajen ganin ta kara inganta tashar tsandauri na garin Onne don kara bunkasa harkokin shigowa da kuma da kaya kasar nan, wanda hakan zai kara habaka tattalin arzikin kasa.

Ministan Sufuri Muazu Sambo Jaji ne ya bayyana haka a garin Onne da ke jihar Rivers, a cigaba da ziyarar aiki na kwanaki Uku da ministan yake gudanarwa don gano dalilan da ya sanya tashar da tsandaurin ba ta yin aiki kamar yadda ya Kamata.

” daga cikin dalilan da suka sanya na kawo wannan ziyarar aikin shine , muna aiki da rundunar sojin ruwa don tabbatar da tsaron hanyoyinmu na ruwa, kuma hukuamar NIMASA ta samar da karin kayan aiki na zamani don ganin mun cimma wancan buri namu” inji ministan

Da yake ministan karin bayani a tashar ajiye sundukai wato containers shugaban hukumar WACT Nigeria Naved Zafa yace a kokarinsu na inganta aiki sun samar da injinan da ke sarrafa sundukai na zamani don cimma nasarar gwamnatin tarraya.

Yace hukumar hana fasakwauri wato customs ta samar da wani sabon na’ura na zamani wanda zai rinka tantance kayan  da Aka shigo da su ko ake shirin fitar da su.

Yana mai cewar sabon na’urar zai taimaka wajen bunkasa kasuwanci da kima tsaro, inda zaa magance shigo da kaya marasa inganci da muggan kwayoyi, da kuma saukaka gudanar da aiki ga jami’ai.

Sauran wuraren da ministan ya duba sun hadar da wuraren tantance kwantaina kashi daban daban dake garin na onne.

Yayin ziyarar minstan ya sami rakiyar direktan kudi na maaikatar Umaru Hassan, wanda ya wakilci babban sakataren maaikatar, sai direktan da ke kula da harkokin sharpieah Pius Oteh da sauran manual jami’an Hukumar