Menu

SHUGABAN HUKUMAR NIMASA YA JINJINAWA MASU RUWA DA TSAKI

Admin 4 years ago

Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan, Dr Bashir Yusuf Jamoh yace masu ruwa da tsaki a harkar kula da iyakokin ruwa na bada gagarumar gudunmawa wajen ciyar da hukumar gaba.

A wata sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin Ikko, yace Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a wajen bikin shagulgulan makon kwastamomi da hukumar ta shirya a shedikwatar ta dake jihar Legas.

Dr Bashir Yusuf Jamoh yace nasarar da hukumar ta samu ta fuskar sayen kadarori, da kuma hannayen jarin da take zubawa a bangarori da dama na da nasaba da gudunmawa da ma’aikatan hukumar da masu ruwa da tsaki ke badawa.

Dr Bashir Jamoh yayi amfani da daman taron inda yayi maraba da Shugabar hukumar kyautata jin dadin kwastamomi ta kasa wato SERVICOM, Mrs Nnenna Akajemeli, inda ya shaida mata cewar yin aiki bisa tsarin tanade-tanaden dokokin hukumar ya taimaka matuka wajen jin dadin alaka tsakanin masu ruwa da tsaki na ciki da wajen hukumar ta NIMASA.

A nata jawabin, Shugabar hukumar kyautata jin dadin kwastamomi ta kasa, Mrs Nnenna Akajemeli ta yaba da irin nasarorin da hukumar ta cimma a bangarori daban-daban, musamman ta fuskar kyautatawa masu ruwa da tsaki a hukumar ta hanyar sauraren koke-koken su da kuma share masu hawaye, inda ta ce ba shakka, hukumar na tafiya daidai da zamani.

Ta kuma yi kira ga sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya da suyi koyi da hukumar NIMASA wajen kyautata alaka da jin dadin masu hulda da hukumar.

An raba kyaututtukan bazata ga wasu daga cikin ma’aikatan hukumar a karshen taron.

Shi dai shagulgulan makon kwastamomi taro ne da ake yi a fadin duniya a makon farko na watan Oktoba duk shekara don nuna muhimmancin da kwastamomi suke da shi.

Manufar bikin shine tabbatar da hadin kai, karfafa gwiwar ma’aikata don zaburar da su wajen aiki da kuma kara wayar da kansu wajen sanin muhimmancin kwastamomi wajen nasarar kowace ma’aikata.