Daga Abdullahi Kano
An Bukaci Matasa da as guji duk wani Nau’I na shaye shayen miyagun kwayoyi da sace sace da kuma yin abota da bata garin abokai.
Dr Hadi Musa da ke Unguwar Tunga , karamar Hukumar Gwale da ke jihar Kano ne ya bukaci hakan lokacin da yake yin jawabi yayin wani taron wayar da kan matasa ta yadda zasu fuskanci irin illar da shaye shayen miyagun kwayoyi ke haifarwa, ga rayuwar Alumma.
Yace ya zama wajibi matasa su rungumi skidar koyon sana’on Dogaro da Kai, su guji zaman kashe wando , wanda a cewarsa hakan na haifar da mutuwar zuciya.
” wannan taron laccar ba itace karo na farko ba, kwanaki munyi makamancin wannan taron , kuma bisa laakari da muhimmancinsa au matasan da kansu suka bukaci a sake shirya musu irin wannan bitar duba da irin dumbin ilmin da suke samu”
Dr Hadi Musa yace matasa su ne ginshikin cigaban kowace alumma don haka ya zama wajibi a hada hannu wuri guda don ganin an jawo matasa a jiki , don ta haka ne zaa fuskanci irin halin da suke ciki don a tallafa must.
Yace kungiyar cigaban alummar tunga tana bibiyar yadda matasa ke gudanar da harkokinsu a unguwar don gudun kada a shigo da wata ta’ada wacce zata gurbata tarbiyar kana nan yara masu tasowa.
Da yake taaliki Alhaji Nasiru Mohammad ya hori matasan da su kaucewa rudin zuciya, da yin abota da yara yan shaye shaye da kuma fadar daba da makamantansu.
” ku San irin wadanda za ku yi abota da su, kada wani ya kawo maka ajiyar waya ko agogo ko want abu Mai tsada ka karba kace zaka ajiye, wannan zai iya jefa ka cikin babbar Matsala , ta yiwu wayar ta sata ce ba ka sani ba”
Yayin taron bitar an gudanar da adduoi don dorewar zaman lafiya a jihar kano da kasa ba ki daya

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
2027: INEC registers 155,133 new voters in Bauchi
Ambassador Dr Amina Namadi Launches Book, Distributes Educational Materials in Jigawa
May Day Without Meaning: The Silence of Empty Pockets
Bichi Moves Motion as Kano APC Stakeholders Endorse Tinubu for 2027, Raise N50m for Nomination Form
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper