Menu

AYYUKAN DAKON KAYA A TEKU NA DA MUHIMMANCI WURIN RAGE CUNKOSO A TASHOSHIN JIRAGEN RUWA– Shugaban NIMASA

Admin 4 years ago

Muna son hada kai da NIMASA – Shugaban BOAN

Babban daraktan hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, Dr. Bashir Jamoh ya bayyana cewa, ingantaccen tsarin tafiyar da harkokin dakon kaya daga teku na da muhimmanci wurin rahe cunkoson ababen hawa akan titunan da suka dangana ya zuwa tashoshin jiragen ruwa a Najeriya.

Shugaban NIMASA ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar masu Damon kaya a teku , Hon. Bunmi Olumekun a babban ofishin hukumar dake Legas.

Jamoh ya ce “Ayyukan sufurin kayayyaki daga teku sun taimaka wajen rage cunkoso a tashar Apapa, saboda suke jigilar kaya sake cikin sundukai (kwantena) daga wannan tashar ruwa na kan tudu zuwa wani, wanda hakan ya rage matsin lamba a kan hanyoyinmu, tare da ba da gudummawar ga ci gaban tattalin arzikin kasa”.

Da yake kara bayani, Shugaban Hukumar NIMASA, ya bukaci ma’aikatan da su zuba jari a bangareb jigilar kaya a jiragen ruwa irin na zamani da za su iya yin gogayya da takwarorinsu na kasashen waje, domin hakan zai taimaka musu su a cigaba da damawa su a maimakon yan kasashen waje su karbe ayyukansu.

A yayin da yake ba su tabbacin hukumar za ta yi duk mai yiwuwa wajen inganta ayyukan jigilar kaya a jiragen ruwa a matsayin hanyar sufurin jiragen ruwa, ya kuma bukace su da su jajirce a fannin horar da mambobinsu, domin hakan zai taimaka musu wajen ganin sun fahimci halin da ake ciki a wannan zamani da kuma karfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

“Haɓaka ƙarfin gwiwa ga ma’aikata yana da kyau ga wadanda suke wannan harka don kasancewa a cikin wadanda ake damawa da su , tare da samun damar yin gogayya yadda ya kamata a kowace fuska. Kasuwancin jigilar kayayyaki yana tafiya ne tare da fasahar zamani, don haka ba za a iya cimma hakan ne ta hanyar samun horo don cigaba da cin gajiyar wannan tsarin sufuri,, ”in ji Jamoh.

Bugu da kari, ya bayyana cewa hukumar ta fara aikin kawar da baraguzan ruwa a fadin kasar nan, bisa ga umarni da amincewar majalisar zartaswa ta tarayya, domin tabbatar da cewa hanyoyin sun kasance ba wata matsala na zirga-zirgar ababen hawa, tare da kaucewa hadurra a kan hanyoyin ruwa. . “Wannan shi ne karo na farko da Hukumar ta dauki cikakken tsarin kawar da tarkacen jiragen a dukkan shiyyoyin dake Legas, Fatakwal da sauran wuraren da jiragen ruwa ke shawagi”.

Tun da farko a jawabinsa shugaban kungiyar masu jigilar kaya a teku, Hon. Bunmi Olumekun ya yaba da kokarin hukumar wajen gudanar da ayyukanta na ci gaba da bunkasa harkokin tekun Najeriya , ya kuma yi alkawarin ci gaba da baiwa kungiyar hadin kai da hukumar wajen ganin an cimma wasu ajandar guda uku na gwamnati mai ci a yanzu.

Hon. Olumekun, wanda ya lura da yadda baki ‘yan kasashen suka yi kaka-gida a ayyukan dakon kaya a jiragen ruwa a Najeriya, ya yi kira ga Hukumar da ta saukaka hanyoyin samun lamuni a kan bashi mara kudin ruwa domin taimakawa masu harkar dakon kaya na jiragen ruwa su mallaki kayan aiki irin na zamani.

Osagie Edward
Mataimakin Darakta, Hulda da Jama’a na NIMASA
edward.osagie@nimasa.gov.ng Maris 29, 2022