-Kudirin GYARA Na DA NUFIN INGANTA ayyukan HUKUMAR, GBAJABIAMILA.
– Ma’aikatar Sufurin na adawa da daukar Kaso 12% na kudin shigar NIMASA don tafiyar da harkokin jami’ar sufurin jiragen ruwa
Shugaban Majalisar Wakilai, Honorabul Femi Gbajabiamila a ranar Talata ya sanar da cewa, Majalisar ta 9 ta fara gyaran dokar NIMASA ta 2007 da kuma Dokar dake sa ido kan jigilar fasinjoji da kaya ta 2003 saboda bukatar inganta ayyukan fannin sufuri tekun Najeriya don magance abubuwan da ke faruwa a yanzu.
Honorabul Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayyana bude taron kwana biyu na kwamitin majalisar kan harkokin tsaron ruwa kan wasu kudurorin da suka shafi sufurin jiragen ruwa a wannan Kasa.
Shugaban majalisar ya lura da bukatar samar da tsarin da ya dace na fannin ruwa ta Najeriya daidai da abubuwan da ke faruwa a lokacin don tabbatar da ana cin gajiyar bangaren ruwa yadda ya dace a Najeriya.
A nata bangaren, shugabar kwamitin majalisar mai kula da harkokin ruwa a teku, Honorabul Linda Ikpeazu, ta ce an shirya taron sauraron ra’ayin jama’ar ne don tabbatar da cewa an dauki matakin da majalisar ta dauka game da kudirorin daga matsayi mai kyau da aka tanadar bisa shawarwarin masu ruwa da tsaki daga dukkan bangarorin da suka jibanci sufurin ruwan.

.
Ta ce: “Sanin kowa ne cewa fannin teku wani tushe ne da kuma samar da ci gaban al’ummomin da ke da arzikin ruwa. Najeriya, ta kowace irin ma’auni, Allah Ya bore mana arziki teku, koguna, da wadatattun halittun ruwa.
“Ba wai kawai mun mayar da hankali ne kan mayar da bangaren tekun wata babbar hanyar samun kudaden shiga da kuma bunkasar tattalin arzikinmu ga raguwar albarkatun man fetur ba, a shirye muke mu bunkasa tattalin arzikin kasarmu, kwatankwacin irin nasarorin da ake samu a yankin tekun da ke sauran kasashen duniya.
A nasa jawabin, mai girma ministan sufuri, Hon. Rotimi Amaechi, ya yabawa Majalisar Dokokin kasar bisa fara nazarin dokokin da suka shafi harkokin ruwa tare da bayyana cewa, sabon kudirin dokar NIMASA da ake nazari a kai, zai kara karfin hukumar wajen daidaita harkokin sufurin jiragen ruwa na Najeriya yadda ya kamata, bisa tsarin da ya dace a duniya.
Ministan wanda ya samu wakilcin Daraktan ma’aikatar shari’a na ma’aikatar Paul Oteh, duk da haka ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda hukumar ke baiwa Jami’ar Maritime ta Najeriya dake Okerenkoko kudade. “Ma’aikatar ba ta goyon bayan kashi 12% na kudaden shigar NIMASA zuwa Jami’ar, wannan shawara a namu ra’ayi kuma ba ta yarda da cewa jami’ar ba kamar sauran cibiyoyin gwamnati da ke karkashin kulawar NUC da ma’aikatar ilimi ta tarayya. Tana da haƙƙin samun kuɗin daga gwamnati kamar yadda Majalisar Dokoki ta kasa za ta keɓe a kowace shekara.” Babban Darakta na NIMASA, Dr Bashir Jamoh, wanda ya samu wakilcin babban daraktan hukumar mai lura da kwadago da dakon fasinjoji da kayansu, Eng. Victor Ochei ya amince da mtsayar ministan a matsayin matsayar NIMASA.
Rundunar sojin ruwan Najeriya a kashin kanta ta goyi bayan gyaran dokar ta NIMASA, inda ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi nazari sosai kan bangaren tsaro na kudirin domin ganin an inganta alaka tsakanin hukumomin biyu.
Babban hafsan sojin ruwa, Awwal Gambo, wanda ya yaba da shirin, ya ce zai inganta ayyukan NIMASA da kuma inganta harkokin tafiyar da harkokin sufurin ruwa a Najeriya.
Gambo wanda ya samu wakilcin Rear Admiral Solomon Agada, ya ce, “samar da wani sashe na daban kan hasarar rayuka a cikin ruwa da kuma shirin kafa sashin binciken hadurran ruwa, zai inganta bin ka’idojin da aka dade ana amfani da su, kamar, dokokin kasa da kasa na hana afkuwar hadurra a yankin teku ta shekarar 1972, wanda kuma yin hakan zai kara samar da kariya ga sufurin jiragen ruwa.”
Kungiyar Mamallaka Jiragen Ruwa ta Najeriya (SOAN), kungiyar kwararru kan sufurin jiragen ruwa ta Najeriya, WISTA, kungiyar kare walwalar ma’aikata sha’anin jiragen ruwa ta Najeriya CIOTA, Kungiyar Ma’aikatan Ruwa ta Kasa da dai sauransu sun kasance masu ruwa da tsaki wadanda suka gabatar da jawabai tare da nuna goyon bayansu ga gyare-gyaren da ake son yi wa dokokin biyu da a yanzu haka ke gaban Majalisar Dokoki ta Kasa.
Osagie Edward
Mataimakin Darakta, Hulda da Jama’a na Hukumar NIMASA
edward.osagie@nimasa.gov.ng
15 ga watan Maris, 2022.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Katsina is Investing Resources to Drive Agriculture Development – governor Radda Tells IsDB Delegation
Over 50 Feared Dead in Suspected Military Airstrike at Borno–Yobe Border Market
After Intense Meetings: Kano APC Stakeholders Nominate Sule Garo As Deputy Governor
APC Legacy Stakeholders Submit Deputy Governorship Nominees to Gov. Yusif
Yusuf Disburses N50,000 Monthly Support to 6,680 Women Across Kano
NSCDC Kano Command Tests Surveillance Drone to Boost Security Operations