Daga Abdullahi Kano
Jamiyyar PRP tace muddin alummar kasar nan su ka ba ta dama ta hanyar zaben ‘ya ‘yanta a mukamai daban daban a shekara ta 2023 to babu shakka zasu sami canji na gaske,wanda zai kai kasar nan tudun mun tsira.
Shugaban jam’iyyar reshen jihar kano Alhaji Abba Sule Namatazu ne ya bayyana hakan yayin wani taro da jam’iyyar ta gudanar a dakin taro na cibiyar nazarin harkokin demokraddiya da ke gidan Mumbayya a kano.
Alhaji Abba sule Namatazu yace jam’iyyar na kan thatttaunawa da ‘yayanta a dukkan sassan kasar nan don farfado da ita,da kuma stara yadda zaa tunkari zabe mai zuwa don lashe dukkanin zabubbukan da ke tafe.

Shugaban jamiyyar yana Mai cewar jamiyyar PRP jam’iyya ce Mai tsantseni da son talakawa, don haka muddin suka sami damar Jan ragamar alumma a kowani mataki to baby shakka alummar kasar nan za us Dara.
Yayi fatan tan jam’iyyar zasu jajirce tare da kara sadaukar da Kai wajen cimma nasarorin da aka sanya a gaba.
A nasa jawabin mai rimon mukamin sakataren jam’iyyar ta kasa malam Kabiru Mohammad Gwangwazo yace lokaci yayi da alummar kasar nan zasu canji na gaskiya, wanda talaka zai gani a kasa musamman ta fuskar inganta tsaro,magance matsalar hauhawar farashin kayan masarufi da tsadar rayuwa wacce ta je fa talaka colon halin kaka nikayi.
Da yake jawabi tun farko kakakin jam’iyyar a kano Alhaji Musa Maigari yace makasudin taron tattaunawar shi ne don a lalubo bakin zaren don ciyar da kasa gaba.
Bisa haka ne ya bukaci alummar jihad kano da na kasa baki daya da suyi fitar farar dango don shiga jam’iyyar ta PRP, inda yace itace jirgin fiton talakawa daga halin da suke ciki.
Taron ya sami halartar shugabbanin jam’iyyar na jihohi, sauran ‘yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki.


Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
2027: INEC registers 155,133 new voters in Bauchi
Ambassador Dr Amina Namadi Launches Book, Distributes Educational Materials in Jigawa
May Day Without Meaning: The Silence of Empty Pockets
Bichi Moves Motion as Kano APC Stakeholders Endorse Tinubu for 2027, Raise N50m for Nomination Form
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper