Menu

NAJERIYA NA SAMUN GALABA A YAKI DA TAKE YI DA FASHIN TEKU – KUNGIYAR TURAI.

Admin 4 years ago

……kamar yadda NIMASA ta jaddada kudirinta na dorewar wannan nasara.

…… Kasashen Japan da Koriya sun tallafawa shirin tsarin teku na DEEP BLUE.

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ta hannun babban jami’inta mai sa ido kan a mashigin gabar tekun Guinea, Amb. Nicolas Martinez, ya yabawa gwamnatin Najeriya kan samar da jagoranci a mashigin tekun Guinea a yakin da ake da aikata laifuka a bangaren teku wanda ya haifar da kyakkyawan sakamako. Yabon ya zo ne a karshen wata ziyarar aiki da tawagar EU ta kai wa hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya, NIMASA, wadda ta duba wasu kayyaki da ake amfani da su karkashin shirin bayar da kariya tsaro ga ruwayen kasa da aka fi sani da deep blue project.

Amb. Martinez ya lura cewa EU ta kasance amintacciya ga yankin gabar tekun Guinea kuma za ta ci gaba da ba da taimako mai yawa da kuma niyya don ƙarfafa muhimman abubuwan da aka Shata a sailin taron tsarin da ya gudana a birnin Yaoundé tare da yaukaka daɗaɗɗiyar dangantaka tsakanin ƙasashe membobin ECOWAS, kamar Najeriya da EU

Ya ce: “Muna goyon bayan shugabancin Najeriya a yunkurin da ake yi na kawo karshen fashin teku da sauran laifukan da ake aikatawa a ruwa. Zaku iya tuntubar EU a kodayaishe saboda muna goyon bayan wannan tsarin tsaro da aka fidda a birnin Yaounde. Muna kira ga Najeriya da ta Samar da bayanai kan nasarorinta ga sauran kasashen yankin domin dakile fashion teku. A bayyane yake daga sakamakon da aka samu ya zuwa yanzu cewa Najeriya, tana ba da jagoranci ga sauran kasashe, tana samun nasara a yakin da ake yi da ‘yan fashin teku.”

Da yake jawabi a wajen liyafar tawagar EU, babban daraktan NIMASA, Dr Bashir Jamoh, ya bayyana cewa hukumar kula da jiragen ruwa ta duniya IMB, ta cire Najeriya daga cikin kasashen sake fama da fashin teku a kwanakin baya ne biyo bayan kokarin hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki a ciki da wajen kasar.

“Ba a yabob Dan kuturu sai ya girma da yatsa”. Yanzu abin da ya fi mayar da hankali gare mu a NIMASA shine dorewar wannan Nasara. Ingantacciyar tattara bayanan sirri da rabawa tsakanin duk masu ruwa da tsaki sun taka rawa sosai a sakamakon da muke gani yanzu. Ya ce: shirinmu na Deep Blue Project, da dokar SPOMO da Majalisar Dokoki ta kasa ta kafa, Hukunce-hukuncen masu aikata laifuka a karkashin dokar SPOMO, jajircewar sojojin ruwa na Najeriya da sauran rundunonin soji na Sojojin Najeriya, tare da una goyon bayan da kasashen duniya suka bayar, duk sun taimaka wurin rage fashib teku a gabar tekun Guinea.

Da yake karin haske, Dr Jamoh ya ce tuni NIMASA ta fara sa ido a kan kokarinta na samun dorewa. Muna aiki kan wani taron dorewar jiragen ruwa na duniya wanda za mu shirya a Abuja nan gaba a wannan shekara; Haka kuma ana kan aiwatar da cikakken tsarin manufofin ruwa na kasa ga Najeriya.

Da yake tsokaci kan shirin na Deep Blue, Dakta Jamoh ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Japan ta yi alkawarin bayar da dala miliyan 2.4 don tallafawa aikin Deep Blue a daidai lokacin da gwamnatin kasar Koriya ta bayar da gudunmuwar jirgin yaki ga NIMASA domin kara yawan jiragen ruwa na Deep Blue Project.

Tawagar da ta hada da Ambasada Martinez, da wasu zababbun kasashe mambobin kungiyar EU, tare da shugaban hukumar NIMASA da manyan ma’aikatan hukumar, sun gudanar da rangadin duba kadarorin Deep Blue Project a makarantar sojan ruwa ta Najeriya. Sun kuma shaida wani atisayen da rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta yi inda aka nuna wasu kayayyakin aikin da ake da su a kasa.

Ma’aikatar Sufuri da Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya ce ta kaddamar da shirin na Deep Blue Project wanda aka fi sani da Integrated National Security and Waterways Protection Infrastructure a yayin da NIMASA ke aiwatar da shi. Babban manufarta ita ce tabbatar da tsaron ruwan Najeriya har zuwa mashigin tekun Guinea.

Osagie Edward

Mataimakin Darakta, Hulda da Jama’a na Hukumar NIMASA

edward.osagie@nimasa.gov.ng
8 ga watab Afrilu, 2022