Shirin Zai Kawo Karshe Ayyukan Batagari A Yankin Tekun Guinea –Jamoh
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanya hannu a kan yarjejeniya da kasar Japan don huldar tattalin arziki da walwalar jama’a da suka hada da samar da kananan jiragen ruwa masu tsananin gudu domin karfafa tsaro a yankunan tekun kasar nan, za a aiwatar da yarjejenyar ne tare da Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NIMASA).
Bayanin haka ya fitio ne a sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulda da Al’umma na hukumar NMASA, Osagie Edward ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai ranar Talata 28 ga watan Yuni 2022.
Sanarwar ta cigaba da cewa, Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Prince Clem Agba ya sanya hannu a madadin Nijeriya yayin da Ambasada Kazuyoshi Matsunaga ya sa hannu a madadin gwamnatin Japan, yayin da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NIMASA), Dakta Bashir Jamoh ya kasance a wurin taron.
Prince Agba ya lura da cewa, samar da jiragen ruwan zai lakume Dala Miliyan 2.78, zai kuma matukar taimaka wajen shirin samar da cikakken tsaro a can cikin teku. Ya yaba wa gwamnatin qasar Japan a kan yadda ta nuna damuwa a bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.
“Wannan shirin zai karfafa ayyukan NIMASA zai kuma kara karfafa dangatakar da ke tsakanin gwamnatin tarayyar Nijeriya dana Japan.”
“Nijeriya na kuma mika godiyarta a kan yarjejeniyar da muka sanya wa hannu kwanaki baya na inganta samar da wutar lantarki a Abuja, da kuma rawar da Japan ke takawa na samar da ingantaccen tsari na dogon zango da zai kai Nijeriya ga tudun-mun-tsira a bangaren samar da bunkasar wutar lantarki a kasar nan”. In ji Ministan.
A nasa jawabin, Darakta Janar na NIMASA Dakta Bashir Jamoh, ya tabbatar wa da gwamnatin kasar Japan cewa, hukumarsa tana aiki da wasu hukumomi za kuma su tsayu wajen ganin ana cigaba da yakar masu fasakwauri a yankin tekun Guinea.
“Muna maraba da shirin samar da kananan jiragen ruwa masu tsananin gudu a kan jerin kayayyakin aikinmu, tabbas zai taimaka wajen kara karfafa aikin samar da tsaro a cikin yankunan teku ba wai a Nijeriya kawai ba har ma a yankin tekun Guinea, musammna ganin kusan kashi 60 na zirga-zirgan da ake yi a yankin ana bi ne ta hanyoyin ruwan Nijeriya “.
“Za mu sanya wadanna kayan aikin a cikin jerin kayayyakin mu na aiki a shirin ‘Deep Blue Project’, inda a halin yanzu muna da manyan jiragen yaki 2, jiragen yaki masu kai farmaki daga sama 2; Jirage masu saukar ungulu guda 3; jiragen sama marasa matuki guda 10; jiragen yaki masu kai farmaki 17; tankunan yaki 16 da kuma cibiyar bibiyar halin da ake ciki na musammam mai suna ‘C4i centre.”
Da ya ke jawabinsa, Ambasada Matsunaga Kazuyoshi ya ce, an samar da shirin ne don tallafa wa irin kokarin da Nijeriya ke yi na yakar batagari masu zagon kasa ga tattalin arzikin Nijeriya, ta haka za a iya dankwafar da ayyukan ‘yan fashi da makami da kuma dukkan ayyukan batagari da ake aikatawa a yankin tekun Nijeriya
Ambasadan ya kuma kara da cewa, “Kamar yadda kuka sani harkokin masu aikata laifukka sai kara karuwa yake yi musamman a yankin tekun Guinea, kuna sane kuma cewa ayyukan na kawo cikas ga bunkasar tattakin arzikin al’ummar yankin wadanda ke fuskantar talauci wanda hakan kuma ke tilasta su fadawa harkokin ta’addanci. Tabass akwai bukatar kawo karshen wannan lamarin.”
“Al’umma da gwamnatin Japan suna fatan wannan shirin zai taimaka wa NIMASA wajen karfafa ayyukanta na tabbatar da tsaro a yankin ruwan Nijeriya wanda hakan zai kara farfado da tsaro a yankin tekun Guinea.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Shekarau Defect to APC After Consultations
Dropping Rurum for Deputy Governor: Gamble Gov Yusuf Cannot Afford – Analyst Warns
Kano APC Reaffirms Support for Tinubu’s Second Term, Disowns Alleged Arewa Forum Statemen
FG Pushes Ahead with Abuja–Kano–Maradi Rail, Sets December Deadline for Key Segments
SPMC Begins Quarterly Oversight of Project Sites, Reviews Progress Across Zone 3