Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Dr Bashir Yusuf Jamoh ya ce hukumar za ta cigaba da aiki tare da cibiyoyi da masu ruwa da tsaki don ciyar da hukumar gaba.
A wata sanarwar da ta samu sa hannun mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie yace Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan kungiyar lauyoyi ta kasa reshen babban birnin tarayya a ofishin shi dake birnin ikko.
Dr Bashir Yusuf Jamoh yayi bayanin cewa aiki da kungiyar da kuma bangaren shari’a ya zama tilas bisa la’akari da batutuwa masu sarkakiya dake tattare da ayyukan hukumar da ke bukatar sasanci.
Ya bukaci hadin kan kungiyar wajen ganin an zartar da hukunce-hukunce da kuma sasanci da suka shafi ayyukan hukumar don masu zuba hannun jari su samu kwarin gwiwa.
Shugaban hukumar har ila yau yayi nuni da cewa hukumar ta NIMASA ta samu nasarar cafke masu aikata laifi a iyakokin ruwan kasar nan da kuma sauran laifuka masu alaqa da haka akan iyakokin ruwan kasar nan.
A cewar Dr Bashir Jamoh, hukumar NIMASA baza ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kan iyakokin ruwan kasar daga masu aikata laifi daban-daban ta hanyar aiki tare da sauran hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya, da na kasashen ketare da kuma sauran masu ruwa da tsaki wajen tsaurara tsaro a kan iyakokin ruwan kasar nan da na tafkin guinea.
Ya kara da cewa hukumar ta kama masu laifi ashirin da uku inda goma a cikin su aka tura sa gidan gyara hali inda zasu shafe shekaru goma kowannen su, yayin da sauran ukun wadanda baqin haure ne aka ci su tara saboda laifukan da suka aikata akan iyakokin ruwan kasar, sannan ya kara da cewa hakan zai zama izina ga sauran masu aikata irin wadannan laifukan.
Dr Bashir Jamoh ya lura da cewa duk da irin nasarorin da hukumar ta samu a bangaren kula da harkokin iyakokin ruwa, hukumar na bukatar cigaba da hadin gwiwa da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki har da bangaren shari’a don cimma manufar da aka sanya a gaba.
Shugaban hukumar ta NIMASA ya bayyana cewa horas da ma’aikata na daga cikin ginshikin gudanar da ayyukan hukumar inda ma’aikata har da na sashin shari’a suke samun horo akai-akai ta fuskoki da dama musamman dokokin da suka shafi ayyukan kula da harkokin iyakokin ruwa a jami’ar kula da harkokin iyakokin ruwa dake kasar Sweden don suyi gogayya da takwarorin su na duniya.
Tunda farko a jawabin shi, Shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa reshen babban birnin tarayya, Mr Adjeh Monday bayyana gamsuwar shi da yabawa hukumar gudanarwa ta NIMASA karkashin jagorancin Dr Bashir Yusuf Jamoh dangane da irin nasarorin da hukumar ta samu inda ya jaddada muhimmancin cigaba da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a fannin kula da harkokin iyakokin ruwa.
Ya kara da cewa kungiyar za ta cigaba da da lalubo hanyoyin hadin gwiwa da za su taimakawa NIMASA a yunkurin ta na cigaba da kare iyakokin ruwan kasar nan.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
2027: INEC registers 155,133 new voters in Bauchi
Ambassador Dr Amina Namadi Launches Book, Distributes Educational Materials in Jigawa
May Day Without Meaning: The Silence of Empty Pockets
Bichi Moves Motion as Kano APC Stakeholders Endorse Tinubu for 2027, Raise N50m for Nomination Form
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper