Babban Sakataren hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya, Mr Kitack Lim ya bayyana cewa Nijeriya na bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban tattalin arzikin duniya.
A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar NIMASA Mr Edward Osagie ya fitar ya ce Mr Kitack Lim ya bayyana hakan ne a wajen liyafa ta musamman da masu ruwa da tsaki a bangaren iyakokin ruwan kasar nan suka shirya mashi a birnin Ikko.
Mr Kitack Lim wanda ya bayyana farin cikin shi dangane da gayyatar da Ministan harkokin sufuri yayi mashi a ziyarar shi ta farko a Nijeriya ya kuma bayyana Nijeriya a matsayin kasa da Allah ya albarkace ta da dimbin arzikin ma’adinai da kuma mutanen kirki inda ya kara da cewa ya samu kyakkyawar alaqa da jama’ar kasar nan a wurare daban-daban a baya.
kARANTA WANNAN:Shugaban Hukumar Nimasa ya Gana da yan kasuwar koriya ta kudu
Babban Sakataren wanda Dan asalin kasar koriya ne, ya bayyana fatan cewa kasar shi da Nijeriya zasu inganta dangantakar dake tsakanin su.
Ministan sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo da babbar sakatariya a ma’aikatar, Dr Magdaline Ajani da shugabannin hukumomin dake karkashin ma’aikatar da kuma masu ruwa da tsaki a bangaren iyakokin ruwan kasar ne suka tarbi babban bakon.
Ana kuma sa ran Mr Kitack Lim zai ziyarci hukumar NIMASA don ganewa idanun shi yanda hukumar take gudanar da ayyukan ta.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
After Intense Meetings: Kano APC Stakeholders Nominate Sule Garo As Deputy Governor
APC Legacy Stakeholders Submit Deputy Governorship Nominees to Gov. Yusif
Yusuf Disburses N50,000 Monthly Support to 6,680 Women Across Kano
NSCDC Kano Command Tests Surveillance Drone to Boost Security Operations
Police Raid Criminal Hideout, Arrest Suspects, Recover Firearm, Illicit Substances in Akwa Ibom
CP Bello Inspects Police Constables Screening Exercise in Gusau