Daga Abdullahi Kakaki
Kungiyar Ciagaban Alummar Unguwar Kakaki da ke birnin zazzau a jihar Kaduna ta Bukaci Maaikata da Mawadata da su rungumi akidar taimakawa matasa masu tasowa don suma su dogara da kawunansu.
Shugaban kungiyar injiniya Shuraihu Ladan Shuraihu ne ya bayyana bukatar hakan yayin taron karawa juna sani da kuma karrama wasu yan Asalin unguwar wadanda suka ba da gudunmuwa wajen cigaban Alummar yankin.
Yace kungiyar matasan Sun Karrama Abdulhameed Mohammed (Babawo) ne wanda babban ma’aikaci ne a hukumar shirya jarrabawa ta NBAIS bisa laakari da irin gudunmuwar da ya bayar, kuma yake kan bayarwa wajen cigaban alummar yankin kakaki, albarkawa, kwangero,kwarbai, da duk sauran anguwannin da ke birnin zazzau.
Adhere to the Ethics of your Profession – Emir Bamalli Charges Journalists
“Muna adduar Allah ya yawaita mana mutane masu kishi da son cigaban alumma irin Alhaji Abdulhameed Babawo a wannan yanki Namu, domin samun karin cigaba da yalwar arziki”
Injiniya Shuraihu Ladan Shuraihu ya kuma shawàrci matasa su rungumi neman ilmi da koyar sanao’i ta yadda zasu zamo masu dogaro da kawunansu, su kuma rinka taimakawa marayu don suma su zama masu Amfani ga alumma baki daya.
Da yake jawabi yayin taron mai girma Na’ibin zazzau malam Mohammad Sani(Kawu Lamido) ya yi kira da a riki zumunchi da son tallafawa marayu, inda yayi dogon jawabi tare da kawo misalai daga nassi na irin falalar da taimakon Maraya ke da shi.
A nasa jawabin sheikh Jibrin Ibrahim Shuraihu ya ja hankalin iyaye kan su kara kula da tarbiyar ‘ya ‘yansu, inda yace kiwo ne Allah Subhanahu wa ta’ala ya baiwa duk wanda yake da ‘ya ‘ya, kuma tabbas Allah zai tambayi yadda aka tarbiyantar da su.
Da yake jawabin Godiya bisa karramawar da kungiyar ta yi masa Alhaji Abdulhameed Mohammed (Babawo) ya godewa Alummar unguwar kakaki bisa karramashi da suka yi.
” na gode kwarai da karramawar da kuka yi min, kuma insha Allah zamu cigaba da bakin kokarinmu wajen cigaba da yiwa alumma Hidima”
Taron ya sami Halartar shugabannin unguwar kakaki , matasa da sauran Alumma.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
2027: INEC registers 155,133 new voters in Bauchi
Ambassador Dr Amina Namadi Launches Book, Distributes Educational Materials in Jigawa
May Day Without Meaning: The Silence of Empty Pockets
Bichi Moves Motion as Kano APC Stakeholders Endorse Tinubu for 2027, Raise N50m for Nomination Form
Yusuf Orders Probe into Alleged N1.5bn Salary Deductions in Kanoi
Fred Itua named Group Politics Editor, The Sun Newspaper