Daga Abdullahi Kano
Tsohon Dan majalisa mai wakiltar kiru da Bebeji a Majalisar wakilai Abdulmumin jibril Kofa , ya kaddamar da kasuwar manoma da cibiyar kasuwanci ta kofa domin bunkasa harkar noma da kasuwanci, a Karamar hukumar Bebeji Dake Kano.
Tsohon Dan majalisar wanda yanzu shi ne dan takarar Kiru da Bebeji a Majalisar wakilai cikin jam’iyyar NNPP a zabe mai zuwa ya gina
Katafariyar kasuwar irinta ta farko a Kano wadda aka kwashe Shekaru goma ana aikinta wacce zata zamo wata hanya ta bunkasa harkokin noma da Kasuwanci da Kuma samarwa matasa aikin yi a kano.

Kasuwar mai dauke da shaguna dari biyu, da masallaci Mai daukar masallata dubu biyar da gidan Mai, da Kuma Babban filin Ajiye manyan motocin tirela- tirela masu daukar kaya da Ajiyewa sama da guda dari.
Da yake yiwa Manema labarai Karin haske game da Kasuwar Abdulmumini kofa ya bayyana cewa kasuwar kasuwa ce da duk abinda ake nema za’a samu, kama daga dakin Hutu, wurin karbar magani, sannan Kuma sun shirya tsaf wajen bada tsaro Mai inganci a wannan kasuwa.
Abdulmumin Jibrin Kofa ya kara da cewar yanzu haka ma’aikata sama da dari biyar ke aiki tukuru a wannan kasuwar Kuma duk da Haka ana sa ran za’a Kara daukar wasu baya ga Waɗanda zasu yi dakon kaya da yaran shago da dai Sauransu .

A nasa jawabin Shugaban kasuwar kayan Abinci dake Dawanau Alh. Murtala Isa cewa yayi sunyi farin ciki da wannan kasuwa da tazo da kyakkyawan tsari, Kuma kasuwar Dawanau zatayi alfari da wannan kasuwa,
Inda yayi masa fatan Alkhairi da fatan masu hannu da shuni da yan Siyasa zasu yi koyi da wannan aikin Alkhairi da cigaban kasa.
A jawabinsa tun da farko shugaban Yan kasuwa na kasa Dakta Bature Abdulaziz ya yabawa tsohon Dan majalisar bisa wannan namijin kokari da yayi, Wanda yace ya halacci bude kasuwanni da dama Amma bai ga Kasuwar da akai mata tsari irin wannan ba.

Taron ya samu halartar manyan mutane, Yan siyasa da suka hadar da Shugaban Majalisar wakilai femi Gbajibiamila da dan takardar Gwamna a jam’iyyar NNPP Abba kabiru Yusuf, da shugaban majalisar malamai Sheikh Abdullahi Pakistan Wanda ya jagoranci sallah juma’a a katafaren masallacin Dake cikin kasuwar ta manoma da cibiyar kasuwanci ta kofa Wanda Abdulmumini kofa ya sadaukar ga mahaifinsa.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Group Endorses Senator Barau for 2027, Cites Development Record in Kano North
How AA Zaura escaped mob attack by miscreant at Farm centre
Police Avert Bomb Threat at Ikot Ekpene Correctional Facility, Recover Explosives
Gov Radda Empowers 1,169 Youths with Skills, Starter Packs
Kano Assembly Confirms Garo as Deputy Governor
Governor Yusuf Condemns Youth Misconduct During First Lady’s Visit, Calls for Moral Renewal