Menu

Ƙungiyar ‘Yan Jarida Na Fafutuka Don a Hukunta Mutumin da Yayi wa Tsohuwar Matarsa ‘Yar Jarida Dukan Kawo Wuƙa

Admin 4 years ago

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta NUJ a jihar Adamawa na fafutukar ganin an hukunta wani mutum tsohon ma’akacin hukumar wutan lantarki ta Najeriya ta PHCN mai suna Malam Ibrahim Aliyu wanda ake zargin yayi wa tsohowar matarsa, Nafisa Vandi dukan kawo wuƙa.

A sanarwar da shugaban ƙungiyar ‘yan jarida a reshen jihar Adamawa, Ishaka D. Dedan ya fitar a jiya Laraba, ya shaida cewa Nafisa Vandi ‘yar jarida ce da ke aiki da kafar yaɗa labarai ta ABC , yace tsohon mijinta wanda korarren ma’akacin PHCN ne yayi mata ɗan karen duka wanda yayi sanadiyar ji mata ciwo don haka suke neman a bi mata haƙkinta a hukunta wanda ake zargin.

Sanarwar ta ce duk da dai ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin, ƙungiyar na fatan ayi masa hukuncin cikin lokaci inda ta neme sauran ƙungiyoyin kare hakkin mata na duniya da su shiga lamarin.