Menu

Yan Majalisu na Shirin Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Kano

Admin 4 years ago

By Mukhtar Khalil

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan majalisar Dokokin Kano na Shirye Shiryen Tsige Shugaban majalisar Dokokin Kano RT Hon Hamisu Ibrahim Chidari, da Mataimakinsa Hon Zubairu Hamza Massu.

Jaridar Politics Digest ta Ruwaito cewar shirin tsige Shugaban Majalisar da Mataimakinsa ya biyo bayan Nuna goyon bayansu ga neman takarar gwamna da tsohon shugaban majalisar RT HON Kabiru Alhassan Rurum ke yi.

jaridar ta politics digest Ta kara da cewar kwamishinan kana nan hukumomi na jihar kano Alhaji Murtala Garo shi ne kashin bayan Shirya wannan lamari na batun tsige shugaban Majalisar.

politics digest tace shugaban Masu rinjaye na majalisar Hon Labaran Abdul Madari,day tsohon shugaban majalisar RT HON Abdulaziz Gafasa na daga cikin ‘yan gaba gaba na shirya wancan kitimurmura.

jaridar ta politics digest tace ana zargin kitumurmurar na faruwa ne bisa umarnin kwamishinan kana nan hukumomi, murtala Garo.

wani dan majalisar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa jaridar politics digest cewar tabbas yan majalisar na kulle kullen tsige shugaban.

“Shirin tsige shugaban da mataimakinsa ya biyo bayan nuna goyon bayansu da Hon kabiru Alhassan Rurum na neman Geamnan Kano.